Wasu ƴan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 2 a Neja, yayin da sojoji suka kashe Kachalla Balla a Kogi

Wakilinmu, Bashar Aminu ya samo cewa ƴan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane biyu a Melehe, ƙaramar hukumar Kontagora, Jihar Neja, yayin da rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe sanannen shugaban ƴan fashi, Kachalla Balla, tare da mayaƙansa a Jihar Kogi.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun zauna a bakin gidan wani babban malamin makarantar sakandare da daren Juma’a suna kwaikwayon mata, kafin daga bisani su cire hijabansu, su kutsa gidan su tafi da malamin mai suna Aminu Runtoje da wata mata Bafulatana.

Kakakin ƴan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce rundunarsu na bincike kan lamarin kafin ta fitar da cikakken bayani.

A gefe guda, rundunar soji ta tabbatar da kashe Kachalla Balla a ranar Alhamis a yayin artabu a Tunga, a wani ɓangare na Operation Egwua da aka ƙaddamar a ranar 1 ga Satumba domin kawar da miyagun laifuka a Kogi da kewaye.

Wata sanarwa daga Laftanar Hassan Abdullahi ta bayyana cewa sojoji sun kuma ƙwace makamai, sun ceto mutane uku, suka kuma lalata maɓoyar ƴan ta’adda, tare da ƙara ƙarfafa ƙwazon dakarun da ke aikin tsaro a yankin.

KogiNeja
Comments (0)
Add Comment