UNICEF da Kirikasamma sun bayar da tallafin kayayyakin kula da lafiya ga PHCs

Ƙungiyar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da Ƙaramar Hukumar Kirikasamma a Jihar Jigawa sun bayar da kayayyakin kula lafiya domin inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan lafiya a cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko a yankin.

Wakilinmu ya tattaro cewa, kayayyakin da aka bayar sun haɗa da gadon haihuwa, zanen gado, kayan aiki na lafiya, matashin kai da sauran su, waɗanda za a rarraba zuwa ƙananan asibitoci a sassan Kirikasamma.

Shugaban kula da lafiya a matakin farko a ƙaramar hukumar, Kabiru Musa, ya ce kayayyakin za su taimaka matuƙa wajen inganta aikin ma’aikatan lafiya.

A yayin miƙa kayan, shugaban ƙaramar hukumar Kirikasamma, Honarabul Muhammad Maji Wakili Marma, ya yi kira ga ma’aikatan lafiya da su tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen rarraba kayayyakin.

Ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi tare da abokan cigaban ƙasa saboda gyaran cibiyoyin lafiya da gina gidajen ungozoma a Kirikasamma da sauran sassan Jihar Jigawa.

Wakilinmu ya samu wannan sanarwar ne daga bakin Alhaji Musa Muhammad, jami’in yaɗa labarai na ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma.

Jigawa
Comments (0)
Add Comment