Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Wakilinmu ya tattaro cewa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gidansu da ke Kaduna, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukaka gado da al’adar mulkin gaskiya da tsarkaka da marigayin ya bari.
Tinubu ya isa gidan ne a ranar Juma’a, inda uwargidan marigayin, Hajiya Aisha Buhari, da ɗansa Yusuf Buhari da sauran danginsa suka tarbe shi tare da wasu abokan marigayin.
Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa, “Mun zo ne domin mu tabbatar muku cewa muna cikin jimami tare da ku. Rashin jikin mutum ba ya nufin asarar ruhinsa. Ruhin da ya bari a tare da mu, shi ne na jajircewa, kishin ƙasa da nuna gaskiya. Za mu ci gaba da tafiya a wannan hanya.”
A cikin jawabinta, uwargidan marigayin, Hajiya Aisha Buhari, ta gode wa shugaban ƙasa bisa kulawar da gwamnatinsa ke nuna musu.
Ta ce, “Ziyarar nan ta kasance babbar jinjina da kuma ta’aziyya gare mu. Ina kuma roƙon Allah ya ba Shugaba Tinubu ƙarfi da ikon ci gaba da tafiyar da amanar gaskiya da marigayin mijina ya bar masa.”
Wakilinmu ya fahimci cewa Tinubu ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati ciki har da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da gwamnonin jihohi da dama.
Tun da farko, Shugaba Tinubu ya halarci ɗaurin auren ɗan Sanata Abdulaziz Yari, Nasirudeen, da amaryarsa Safiyya Shehu Idris, a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.
An tabbatar da biyan sadakin Naira miliyan ɗaya kafin ɗaurin auren da manyan malamai suka jagoranta.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook