Tinubu ya kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a Rivers, ya mayar da Fubara da ƴan majalisu kan mulki

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a Jihar Rivers, tare da mayar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da kuma mambobin Majalisar Dokokin jihar su ci gaba da gudanar da ayyukansu daga ranar 18 ga Satumba, 2025.

Wannan mataki ya zo ne bayan shafe watanni shida tun daga watan Maris, lokacin da Gwamnatin Tarayya ta kafa dokar ta-baci a jihar, sakamakon rikici mai tsanani tsakanin ɓangaren zartarwa da majalisa wanda ya haifar da tsayawar gudanar mulki.

Wakilinmu ya tattaro cewa a wancan lokaci, majalisar dokokin jihar ta rabu gida biyu, inda ƴan majalisa huɗu suka tsaya kan goyon bayan gwamna, yayin da 27 suka mara baya ga kakakin majalisar Martins Amaewhule, lamarin da ya hana gabatar da kasafin kuɗi da kuma gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Shugaba Tinubu ya ce, “A matsayina na shugaban ƙasa, zai zama babbar gazawa idan ban ɗauki matakin kafa dokar ta-ɓaci ba, domin doka ta bai wa shugaban ƙasa cikakken iko ya tsoma baki a lokutan da ake samun rikicin da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron jama’a.”

Shugaban ƙasan ya ƙara da cewa, matakin ya zama wajibi ne saboda hanyoyin samun tattalin arziƙin jihar, musamman kamar su bututun man fetur, sun fara shiga barazana ta hanyar lalacewa da kai mu su hari, yayin da rikicin siyasa ya tsananta har kotun ƙoli ta bayyana cewa babu gwamnatin da ke aiki a Rivers.

Tinubu ya jinjinawa Majalisar Tarayya saboda amincewa da matakin, tare da godewa sarakunan gargajiya da jama’ar jihar bisa jajircewa da haƙuri da suka nuna tsawon lokacin dokar ta-ɓacin.

Duk da cewa akwai ƙorafe-ƙorafe sama da guda arba’in da aka shigar a kotunan Abuja, Port Harcourt da Yenagoa domin ƙalubalantar kafa dokar ta-ɓacin, shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a matsayin tafiyar demokaraɗiyya, inda ya ce yanzu rahotanni sun nuna cewa shugabannin siyasa a Rivers sun nuna sabuwar alamar fahimtar juna da shirin komawa tafarkin mulkin demokaraɗiyya.

Tinubu ya yi kira ga dukkan gwamnonin jihohi da majalisunsu da su tabbatar da gudanar da mulki cikin lumana da kyakkyawan haɗin kai, domin jama’a su mori cikakkiyar ɗemokaraɗiyya a Najeriya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Bola TinubuRiversSiminilayi Fubara
Comments (0)
Add Comment