Hedikwatar Tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa za ta ci gaba da bin ƙa’idar dole sai jami’i ya yi aƙalla shekaru 15 kafin ya yi murabus daga aikin soja, duk kuwa da hukuncin kotu da ya soke wannan doka.
A ranar Talata, Kotun Ma’aikata ta Ƙasa a Abuja ta yanke hukunci a kan wannan ƙa’ida a shari’ar Flight Lieutenant J.A. Akerele da rundunar sojin sama, inda Mai Shari’a Emmanuel Subilim ya bayyana ƙa’idar a matsayin “bautarwar zamani a ƙarƙashin sunan hidima ga ƙasa” tare da jaddada cewa ba za a tilasta wa wani ɗan ƙasa zama a aikin da ba ya so ba.
Da yake ganawa da ƴan jarida a Abuja a ranar Alhamis, Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya jaddada cewa, “Sai dai idan an sake rubuta ƙa’idojinmu, har yanzu za mu ci gaba da abin da ke cikin takardunmu na HTACOS.”
Ya bayyana cewa sharaɗin shekaru 15 na bambanta ne gwargwadon irin hanyar shiga aikin soja – daga masu shiga ta depot, cadet na NDA, zuwa waɗanda aka ɗauka kai tsaye ta shirin Direct Short Service.
Wannan lamarin dai na ƙara tayar da hankali a rundunar sojan Najeriya a daidai lokacin da matsalolin walwala da rashin albashi mai kyau suka yi ƙamari, abin da ƙwararru suka ce zai iya janyo ƙaruwar ɓacin rai a tsakanin matasan sojoji tare da kira na sake duba yanayin aikin soja a ƙasar.