Shugaban tsagin NNPP a Kano ya ce korar da aka yi wa Kofa “ba ta halatta ba” kuma “ba ta da wani tasiri a doka”

Shugaban wani tsagi na NNPP a Kano, Sanata Mas’ud El’Jibrin Doguwa, ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa daga jam’iyyar, yana bayyana ta a matsayin wadda “ba ta halatta ba” kuma “ba ta da wani tasiri a doka”.

Wakilinmu ya tattaro cewa, Doguwa ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan wani tsagin jam’iyyar mai biyayya ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da korar Kofa bisa zargin yi wa jam’iyya zagon ƙasa.

“Ni ne shugaban jam’iyyar na gaskiya. Wannan hukunci an yanke shi ba tare da saninmu ba, don haka ba shi da wani tasiri,” in ji Doguwa, wanda ya kare Kofa kan wani shirin talabijin da ya jawo hayaniya a ƴan kwanakin nan.

“Abin da Kofa ya faɗa ba ya nuna zagon ƙasa. Kowane ɗan siyasa na da damar sauya jam’iyya. Ko shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taɓa sauya jam’iyya kafin ya shiga wadda yake ciki a yau,” in ji shi.

Doguwa ya zargi Dungurawa da wuce gona da iri, yana gargaɗin ɗaukar matakin shari’a idan ba a dakatar da korar jiga-jigan jam’iyyar ba.

“Idan Dungurawa bai daina wannan abin da ba shi da halaccin yi ba, za mu haɗu da shi a kotu,” in ji shi.

Lamarin dai ya ƙara nuna yadda NNPP ke ta fama da rikicin shugabanci tun bayan zaɓen 2023, yayin da ɓangarori ke fafutukar riƙe iko a Kano kafin fafatawar siyasa mai zuwa.

NNPP
Comments (0)
Add Comment