Saudiyya ta saki alhazan Najeriya da aka cafke da zargin safarar miyagun ƙwayoyi bayan gwamnati ta sa ba ki

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta tabbatar da sakin wasu alhazan Najeriya uku da hukumomin Saudiyya suka tsare tun watan da ya gabata bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Wakilinmu ya tattaro cewa kakakin hukumar, Mista Femi Babafemi, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja ranar Laraba, inda ya ce sakin ya biyo bayan tattaunawa tsakanin NDLEA da gwamnatin Saudiyya.

“An saki Maryam Hussain Abdullahi, Bahijja Abdullahi Aminu da Abdulhamid Saddieq, waɗanda aka tsare na tsawon makonni huɗu. Zai yiwu su iso gida nan ba da daɗewa ba,” in ji Babafemi.

Ya yi gargaɗin cewa ya zama wajibi ga matafiya su tabbatar an sanya musu sunayensu a kan kayayyakinsu yadda ya dace kafin tashin jirgi, don guje wa sharrin masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Cafke Shugaban Ƙungiyar Masu Safarar Ƙwayoyi

Rahoton ya ce a watan Agusta NDLEA ta cafke wani mutum mai shekara 55 da aka bayyana da sunan Mohammed Abubakar, wanda aka fi sani da Bello Karama, bisa zargin shugabantar wata ƙungiya da ta yi amfani da filin jirgin sama na Kano wajen saka miyagun ƙwayoyi cikin kayayyakin wasu alhazai ba tare da saninsu ba.

Babafemi ya bayyana cewa binciken hukumar ya gano wasu ma’aikatan kamfanin SAHCOL sun taimaka wajen sanya ƙarin jakunkuna shida a kan sunayen waɗannan alhazai uku.

Daga cikin jakunkunan, uku na ɗauke da miyagun ƙwayoyi.

“An sanya waɗannan jakunkuna da sunayen waɗannan alhazan ba tare da yardarsu ko saninsu ba. Shugaban ƙungiyar ya tashi da wani jirgi na Egypt Air, yayin da abokan harƙallarsa suka saka jakunkunan a jirgin Ethiopian Airlines,” in ji shi.

Babafemi ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda aka gano da hannu a cikin lamarin su ne Abdulbasit Adamu, Murtala Olalekan, Celestina Yayock da Jazuli Kabir.

An gano shaidar kuɗin da aka biya su a matsayin lada.

Ƙoƙarin Gwamnati

Babafemi ya bayyana cewa shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (rtd.), ya gabatar da cikakken bincike ga hukumomin Saudiyya, tare da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da wasu ministoci.

“A ranar 14 ga Satumba an saki mutum na farko, sai kuma sauran biyu a ranar 15 ga Satumba 2025,” a tabbatarwar Babafemi.

Janar Marwa ya yaba wa jami’an Saudiyya bisa bin yarjejeniyar haɗin gwiwa, tare da gode wa shugaban ƙasa da sauran manyan jami’an gwamnati bisa tallafin da suka bayar.

Lamarin ya haifar da damuwa kan tsaron filayen jiragen sama a Najeriya, inda hukumomi suka ce za su ƙara tsaurara matakan tsaro a Kano don guje wa maimaituwar lamarin.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

AlhazaiMiyagun KwayoyiNDLEASaudiyya
Comments (0)
Add Comment