Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Rundunar ƴan sanda ta Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƴan Sanda, CP Dahiru Muhammad, ta bayyana cewa tana ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da muhimman masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Rahotannin da wakilinmu ya tattaro daga sanarwar rundunar sun nuna cewa, a ranar 10 ga Satumba, 2025, ƙungiyar Awareness for Human Rights and Charity Development, reshen Jigawa, ƙarƙashin jagorancin Kwamared Mohammad Ali, ta kai ziyara ta girmamawa ga Kwamishinan Ƴan Sanda a Hedikwatar Rundunar dake Dutse.
A yayin wannan ziyara, shugabannin ƙungiyar sun bayyana manufofinsu guda uku da suka haɗa da wayar da kan jama’a, kare haƙƙin bil’adama da kuma aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba.
Haka kuma, a rana ɗaya, al’ummar Kudancin Kaduna mazauna jihar sun ziyarci Kwamishinan Ƴan Sandan inda suka bayyana jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tare da bayar da tabbacin ci gaba da bai wa rundunar bayanai masu amfani da sauran goyon baya don tabbatar da tsaro a jihar.
Bugu da ƙari, a ranar 11 ga Satumba, 2025, Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, ASP Ibrahim Sunusi Idris, ya wakilci Kwamishinan Ƴan Sanda wajen taron shekara-shekara na ƙungiyar Nigerian Association of Criminology and Security Studies (NACSS), reshen Jami’ar Tarayya Dutse.
A wajen taron, ASP Idris ya gabatar da jawabi kan taken taron “Media and Crime Reporting”, tare da bayyana muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen ba da sahihan rahotanni kan harkokin laifi.
Haka kuma, ya miƙa kyautar yabo ga shugaban Tsangayar Fasahar Ƙirƙira da Kimiyar Zamantakewar Al’umma, Dr Ahmad Aliyu, a madadin ɗalibai.
Da yake mayar da martani kan waɗannan ci gaban, CP Dahiru Muhammad ya nuna godiyarsa ga ƙungiyoyin da suka kawo ziyarce-ziyarcen, inda ya ce, “Runduna tana daraja duk wata haɗin gwiwa da mutane, al’ummomi da ƙungiyoyi da ke da manufofi na samar da zaman lafiya, adalci da ci gaba. Waɗannan ziyarce-ziyarcen shaida ce cewa tsaro alhaki ne na kowa da kowa. Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi tare da gina amincewa tsakanin jami’anmu da jama’a.”
Kwamishinan ya ƙara da kiran dukkan mazauna jihar da su yi koyi da irin wannan goyon baya ta hanyar bayar da bayanai masu amfani da kuma yin aiki tare da jami’an tsaro domin cimma burin zaman lafiya mai ɗorewa.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook