Rigimar da ta shafi dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta sake ɗaukar sabon salo a jiya Talata, yayin da jam’iyyar PDP da wasu manyan lauyoyi (SANs) suka soki matakin Majalisar Dattawa na ƙin barin ta koma majalisa bayan cikar dakatarwar watanni shidan da aka yi mata.
Wakilinmu ya gano daga wata wasiƙa da Muƙaddashin Magatakardar Majalisar Ƙasa, Dr. Yahaya Danzaria, ya aikewa Akpoti-Uduaghan a ranar 4 ga Satumba, inda aka shaida mata cewa dakatarwarta da ta fara sanya ranar 6 ga Maris, 2025, na nan daram har sai kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan ƙarar da ta shigar da Majalisar Dattawa.
Wannan ya tarwatsa fatan Akpoti-Uduaghan, wacce, a cewar lauyanta, Victor Giwa, ta fara shirin komawa ofis bayan ta kammala watanni shida na hukuncin.
An dakatar da ita ne bayan majalisar ta amince da rahoton kwamitin ladabtarwa, kyautata halaye da karɓar ƙorafe-ƙorafe wanda ya zarge ta da rashin biyayya bayan ta ƙi yarda da canjin kujerar da aka yi mata a majalissar.
Akpoti-Uduaghan ta yi iƙirarin cewa dakatarwarta siyasa ce kawai, tana danganta ta da ƙarar da ta shigar kan zargin cin zarafin neman yin lalata da ita wadda ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio – zargin da majalisar ta yi watsi da shi.
Ta maka majalisar a kotu, inda ta bayyana a watan Afrilu cewa, ta samu hukuncin da ya ba ta nasara, sai dai shugabancin majalisar ya nace da cewa ta ci gaba da zama a dakatarwar har sai watanni shida sun cika.
Jam’iyyar PDP ta bayyana a wata sanarwa daga mai magana da yawunta na ƙasa, Debo Ologunagba, cewa matakin majalisar, “Ƙoƙari ne na APC mai mulki na murƙushe muryar adawa da kuma hana mutanen Kogi ta Tsakiya wakilci a majalisa, wanda yake take Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa da dokokin majalisa.”
Babban Lauyan Najeriya, Adedayo Adedeji (SAN), ya bayyana cewa bai dace a hana sanatar komawa ba, ganin cewa lokacin dakatarwar ya ƙare.
“Dakatarwa ta wucin gadi bai kamata ta yi tasiri wajen hana wakilci ga mazaɓu ba. Kamar yadda Sashe na 68 na Kundin Tsarin Mulki ya fayyace, kujerar majalisa za ta zama wani abu ne kawai a yanayin da kundin ya bayyana kai tsaye,” in ji shi.
Shi kuma Wale Balogun (SAN) ya ce, “A gaskiya, majalisar dattawa ta nuna rashin adalci. Natasha ta kammala watanni shida. An dakatar da ita na wani lokaci. Lokacin ya wuce, dole ne a bari ta koma bakin aiki. Kotun na iya yanke hukunci kan sahihancin dakatarwar, amma wakilcin mutanen Kogi ta Tsakiya bai kamata a ci gaba da hana su ba.”
Haka kuma, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) ya bayyana matakin majalisar dattawan a matsayin “ƙetare iyaka” da kuma “ɗaukar fansa.”
“Dakatarwar watanni shida ce, ta ƙare. Ba tare da sabon ƙudiri daga majalisa ba, hana ta komawa kamar tsawaita dakatarwa ne ba bisa doka ba. Wannan zai nuna rashin dattako da rashin biyayya ga tsarin demokaraɗiyya,” in ji shi.
Sai dai, Mike Ozekhome (SAN), ya ce ya kamata ɓangarorin biyu su jira hukuncin kotu kan ƙarar da ke gudana.
Ƙungiyar SERAP ta soki matakin a wata sanarwa da ta fitar jiya, inda ta ce, “Majalisar Dattawa dole ta bar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma majalisa nan take. Babu doka Najeriya da ke hana ta komawa yayin da shari’a ke gudana. Hana ta aiki, take tsarin mulki ne da take haƙƙin ɗan adam.”