Rahoto ya fallasa yanda ƴan sanda sama da 100,000 ke bauta wa Manya a Najeriya, an bar talakawa cikin ƙarancin tsaro

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Sabon rahoton da Hukumar Ba da Mafaka ta Tarayyar Turai (EUAA) ta wallafa a Nuwamba 2025 ya nuna cewa sama da jami’an ƴan sanda 100,000 a Najeriya an tura su ne domin kare manyan ƴan siyasa da fitattun mutane (VIPs), lamarin da ke rage tsaron al’ummar ƙasa baki ɗaya.

TIMES HAUSA ta tattaro daga rahoton cewa Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa (NPF) tana da jami’ai 371,800 kacal, duk da cewa tana hidima wa ƙasa mai mutane miliyan 236.7 a ƙiyasin 2024.

Rahoton ya ce ana ƙara tsananta giɓin jami’an tsaro saboda yawan tursasa ɗaukacin jami’an zuwa ayyukan VIP maimakon kula da al’umma da hana aikata laifuka.

Rahoton ya bayyana cewa, “Akwai rahotanni tun daga baya-bayan nan da hatta daga 2007 da ke nuna cewa NPF tana da adadin jami’ai 371,800. Fiye da 100,000 daga cikinsu an tura su ne wajen kare ƴan siyasa da manyan mutane, ba al’umma ba.”

Rahoton ya ƙara nuna cewa ƙarancin kaya, rashin nagartaccen tanadi da cin hanci suna jawo jinkirin amsa kiran gaggawa da barin al’ummomi ba tare da kariyar doka ba.

“Ƙarancin ma’aikata, cin hanci da ƙarancin kayan aiki sun haifar da jinkirin amsa kiran gaggawa da barin al’ummomi da dama ba tare da kariya ba.”

Haka kuma rahoton ya ce, “Rashin ingantattun matakan ladabtarwa ya haifar da rahotannin kama-karya, karɓar rashawa da amfani da ƙarfin tsiya fiye da kima.”

Umarnin janye ƴan sanda daga ayyukan VIP

TIMES HAUSA ta tattaro cewa tun bayan hawansa ofis a 2023, Sufeto Janar Kayode Egbetokun ya umarci a janye ƴan sanda na Mobile Police Force daga aikin VIP, yana mai cewa za su mayar da su ga manyan ayyukan tsaro.

A Afrilu 2025 ma ya sake bayar da umarnin janye jami’an MOPOL gaba ɗaya daga VIPs ɗin, amma rahoton EUAA ya nuna cewa wannan doka ba ta sauya halin da ake ciki ba a Najeriya.

A watan Agusta, hadimar shugaban ƙasa kan manufofi, Hadiza Bala-Usman, ta buƙaci a dakatar da wannan tsarin, tana mai cewa hakan ya na rage tsaron ƙasa.

Ta ce, “Muna ganin VIPs suna zuwa da manyan jerin gwanon ƴan sanda, amma yankunan da ke buƙatar tsaro ana barinsu babu komai. Ba za mu cigaba da amfani da jami’an da aka horas domin yaƙi da ta’addanci wajen kare wasu a Ikoyi ba.”

Ta kuma kara da cewa, “Duk wanda ke buƙatar tsaron musamman ya tafi ya ɗauko kamfanin tsaro mai zaman kansa, ba ya ɗau Mobile Police ba.”

Ta buƙaci a sake duba dokar ƴan sanda domin baiwa kamfanonin tsaro damar ɗaukar wasu daga cikin ayyukan da ake loda wa ƴan sanda a Najeriya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

NajeriyaTsaroyan sanda
Comments (0)
Add Comment