PDP zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun da ya dakatar da taron Convention

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta umarci lauyoyinta da su gaggauta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke wanda ya dakatar da gudanar da taron gangamin jam’iyyar da aka shirya yi a ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwambar nan.

Kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, jim kaɗan bayan labarin umarnin kotun ya karaɗe kafafen yaɗa labarai.

Ya ce, “PDP wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa a Najeriya mai bin doka da oda, ta umarci lauyoyinta su ɗauki matakan gaggawa na ɗaukaka ƙara domin kare tsarin dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama a ƙasarmu.”

TIMES HAUSA ta tattaro cewa Mai Shari’a James Omotosho na kotun tarayya dake Abuja ne ya bayar da umarnin a dakatar da taron gangamin saboda rashin cika ƙa’idojin kundin tsarin mulkin ƙasa, na hukumar INEC da na jam’iyyar kanta.

Kotun ta ce PDP ta kasa gudanar da sahihan tarukan jihohi kafin shirya babban taron ƙasa, sannan ta umurci jam’iyyar da ta cika sharuɗɗan da suka wajaba ciki har da bayar da sanarwar kwana 21 kafin ta ci gaba da shiri.

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da shugabannin jam’iyyar na jihohin Imo da Abia da kuma sakataren yankin kudu maso kudu – waɗanda ake alaƙantawa da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Duk da haka, a baya, ranar 9 ga Oktoba, wata kotu ta ƙi bayar da hukuncin wucin-gadi na dakatar da taron.

A martaninsa, Mista Ologunagba ya bayyana hukuncin a matsayin “hari ga tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya,” yana mai cewa ba zai hana jam’iyyar shirya taronta ba.

Ya ƙara da cewa, “Hukuncin bai hana mu ci gaba da shirye-shiryen zaɓen sabbin shugabanni ba, domin kotun ƙoli ta tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa suna da ikon gudanar da harkokinsu na cikin gida.”

PDP ta kuma buƙaci mambobinta su ci gaba da kasancewa masu jajircewa wajen shirye-shiryen gangamin ƙasar mai zuwa.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

ConvetionPDP
Comments (0)
Add Comment