OPay ya ƙaddamar da tallafin karatu na miliyoyin nairori da ɗaliban BUK, ɗalibai za su samu ₦300,000 duk shekara

Kamfanin OPay Digital Services Limited ya ƙaddamar da wani shirin tallafin karatu na Naira miliyan 60 ga ɗaliban Jami’ar Bayero da ke Kano, a ranar Talata, 9 ga Satumba 2025.

Wakilinmu ya gano cewa an ƙulla wannan yarjejeniya ne ta hannun Shugaban Jami’ar, Farfesa Haruna Musa, wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar yin aiki tare (MoU).

Shirin ya samu nasara ne da haɗin gwiwar ƙungiyar ɗalibai (SUG) ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Abdullahi Usman Baba, tare da haɗin kan ƙungiyar NANS.

A jawabinsa, Farfesa Musa ya yabawa kamfanin OPay saboda zaɓar BUK cikin jami’o’in da za su ci gajiyar shirin, yana mai cewa, “Wannan tallafi zai ƙara ƙarfin gwiwar ɗalibai. Ina kira ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da damar yadda ya kamata.”

Shi ma Manajan al’amuran zamantakewar al’umma na kamfanin, Mista Itoro Udo, ya bayyana cewa OPay na da sama da masu amfani da shi miliyan 16 a Najeriya, tare da ƙudirin tallafawa matasa ta hanyar ilimi.

Ya ce BUK na daga cikin jami’o’i 20 da aka zaɓa domin shirin, inda ɗalibai 20 za su riƙa samun tallafin Naira 300,000 kowanne a kowace shekara tsawon shekaru goma.

Daraktan harkokin ɗalibai na jami’ar, Farfesa Shamsuddeen Umar, ya bayyana shirin a matsayin “na kan gaba wajen taimakawa ɗalibai,” musamman ma a wannan lokaci da da yawa ke fama da matsalar kuɗi wajen ci gaba da karatunsu.

BUKOpay
Comments (0)
Add Comment