Gwamnatin jihar Jigawa ta samu yabo daga Ofishin Birtaniya na Harkokin Ƙasashen Waje (FCDO) da Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) bisa yadda ta ke jagoranci wajen yaƙi da ƙarancin abinci da kuma gina makarantu da cibiyoyin lafiya masu jure matsalolin yanayi.
Wakilinmu ya tattaro cewa, yabon ya biyo bayan ƙaddamar da shirin UK–Nigeria Climate Resilience Infrastructure for Basic Services (CRIBS) a garin Chamo, Dutse, ranar Litinin, inda manyan jami’an UNICEF da FCDO suka kai ziyarar ban girma ga Gwamna Malam Umar Namadi a gidan gwamnati.
Cynthia Rowe ta FCDO ta ce, “Muna da haɗin gwiwa na shekaru 20 da Jigawa, kuma wannan shiri zai ƙara ƙarfin jihar wajen jure sauyin yanayi.”
Haka kuma, Wafaa Saeed Abdellatef ta UNICEF ta bayyana Jigawa a matsayin “jiha abin koyi” a fannin abinci, tsabtace muhalli, da jure sauyin yanayi.
Gwamna Namadi ya bayyana yadda jihar ta sha fama da ambaliya, tana lalata makarantu, asibitoci da hanyoyi, tare da kawo cikas ga ilimi da lafiya.
Ya ce matakin farko na CRIBS ya gyara fiye da makarantu da asibitoci 90 a ƙananan hukumomi uku, kuma gwamnati za ta faɗaɗa shirin zuwa ƙarin yankuna.
“Mun yaba ƙwarai da FCDO da UNICEF kan wannan tallafi mai inganci,” in ji gwamnan, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tare da abokan hulɗa wajen kare muhalli da inganta rayuwar yara da al’umma baki ɗaya.