NULGE ta zaɓi sabbin shugabanni a ƙananan hukumomin Jigawa

Wakilinmu ya samo rahoton cewa Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE) ta kammala gudanar da zaɓen sabbin shugabanni a wasu ƙananan hukumomi a Jihar Jigawa, bayan ƙarewar wa’adin tsofaffin shugabannin reshen ƙungiyar a yankunan.

Sabbin shugabannin da aka zaɓa sun haɗa da Haruna M. Mamman a Kirikasamma, Aminu Tafida a Malam Madori, da Ibrahim Maigari a Birniwa.

Wakilan NULGE na jiha, Comrades Aleru Suleman, Docas Garba, da Ibrahim Muazu Maigatari, sun sa ido kan zaɓen, inda suka yaba da yadda aka gudanar da shi cikin lumana, gaskiya da haɗin kai, tare da bai wa mata dama a jerin shugabannin.

A cewar bayanan da aka tattara daga Alhaji Musa Muhammad, Jami’in Yaɗa Labarai na Malam Madori da Kirikasamma, sabbin shugabannin sun yi alƙawarin kawo sauye-sauye masu amfani da kare muradun ma’aikatan ƙananan hukumomi.

Shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa, Salisu Sani Garun-Gabas (Malam Madori), Muhammad Maji Wakili Marma (Kirikasamma) da Shehu Baba (Birniwa), sun taya sabbin shugabannin murna, tare da kiran su da su ƙarfafa ma’aikata wajen tsayawa tsayin daka a bakin aiki domin tallafawa nasarar shirin manufofi 12 na Gwamna Umar Namadi.

NULGE
Comments (0)
Add Comment