Wakilinmu ya tattaro daga Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) cewa, a yayin bikin Ranar Ƙasa da Ƙasa ta Ƙarfafa Ilimi ta 2025, an yi kiran a rungumi ilimi a matsayin mabuɗin ɗorewar ƙasa, haɗin kan al’umma da kuma fitar da miliyoyi daga talauci.
Darakta Janar na NOA, Malam Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce wannan rana ta bana wata dama ce ta tunani kan rawar da ilimi ke takawa wajen rage talauci, bunƙasa koyon rayuwa mai kyau da samar da ƙasa mai daidaito da haɗin kai.
Issa-Onilu ya jaddada cewa, “Ilimi ba kawai iya karatu da rubutu ba ne; ƙofa ce zuwa ga ilimi, ƙirƙira da shiga harkokin demokaraɗiyya cikin girmamawa.”
Ya yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin al’umma, masu tsara manufofi da kungiyoyin farar hula su haɗa kai wajen ƙarfafa ilimi a matsayin hakkin kowa.
Ya kuma ƙarfafa cewa a ƙarfafi ɗakunan karatu na jama’a da na unguwanni tare da saka jari a ƙwarewar zamani (digital literacy) don shirya ‘yan ƙasa ga tattalin arziƙin ƙarni na 21.
“A ƙasar da kowa ya iya karatu da samun fahimta, ƙasarmu za ta fi ƙarfi. Mu mayar da karatu da koyon rayuwa abin alfahari a matsayin al’ada,” in ji shi.