NNPP ta kori ɗan majalisar wakilanta, tana zarginsa da yi wa jam’iyyar APC aiki

Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a Kano ta kori ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a Majalisar Tarayya, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin yin aiki da jam’iyyar adawa da kuma kasa biyan kuɗaɗen jam’iyya na ƙa’ida.

Wakilinmu ya tattaro cewa shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Hashim Dungurawa ne ya sanar da haka a Kano ranar Asabar yayin wani taron manema labarai.

Dungurawa ya zargi Jibrin da “yi wa jam’iyya zagon ƙasa” tare da “bayyanar da biyayya a bainar jama’a ga wasu masu adawa da NNPP”.

Ya ce, “Tuhumarsa ta hanyar tattaunawa ba ta isa ba, sai ma ƙara yi wa amanarmu illa. Shi ya sa muka kore shi. Ba shi da abin da zai ƙara mana.”

Shugaban jam’iyyar ya ƙara da cewa Jibrin ya daɗe bai biyan kuɗin jam’iyya ba.

“Za mu kai shi kotu domin dawo da abin da jam’iyya ke bin sa. Tsarin mulkin jam’iyya ya tanadi biyan kuɗi, amma shi ya ƙi biya,” in ji shi.

Game da fargabar cewa dawowar Jibrin cikin APC na iya rage ƙarfi ga NNPP, Dungurawa ya jaddada cewa Kwankwasiyya ba za ta raunata ba.

“Da shi da gaske yana da ƙarfi, da tuni ya ci zaɓe ai a APC, amma ya faɗi. Sai da ya shiga NNPP ta hanyar Kwankwasiyya ne ya samu wannan kujerar, yanzu yana yaudarar kansa ne,” in ji shi.

Jibrin, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Darakta Janar na Bola Tinubu Support Groups, ya koma Kwankwasiyya a shekarar 2022, inda ya sake samun kujerar majalisar.

Korar tasa ta sake jefa siyasar Kano cikin yanayin ruɗani a yayin da manyan jam’iyyu ke shirin tunkarar manyan zaɓukan 2027.

NNPP
Comments (0)
Add Comment