NLC Ta Cika Alƙawari, Ma’aikata Sun Fito Zanga-zangar Ƙasa Kan Matsalolin Tsaro

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) da rassanta sun gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar Laraba domin nuna adawa da taɓarɓarewar tsaro a Najeriya.

Ƙungiyar ta sanar da shirya zanga-zangar ne tun ranar 17 ga Disamba, tana mai cewa halin tsaro a ƙasar nan “yana ƙara taɓarɓarewa.”

A wata sanarwa da ta aikewa dukkan rassanta na jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa da aka yi ranar 4 ga Disamba, NLC ta yi Allah-wadai da ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Ƙungiyar ta nuna damuwa matuƙa kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana a Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, tana mai caccakar janye jami’an tsaro daga makarantar kafin faruwar lamarin.

Ganawar Tinubu da ƴan Ƙwadago

A ƙoƙarin daƙile zanga-zangar, Shugaba Bola Tinubu ya gana da shugabannin NLC da wasu gwamnonin jihohi a daren Talata, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Imo, Hope Uzodimma.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya shaida wa manema labarai cewa za a sake ganawa da shugaban ƙasar a watan Janairu domin tattauna matsalar tsaron rayuwar ma’aikata da tattalin arziƙinsu a Najeriya.

“Mun tattauna batun tsaro da kuma tsaron kuɗi, domin ma’aikacin da ba ya samun isasshen albashi da abinci na fuskantar matsaloli fiye da sauran,” in ji Ajaero.

Ya ƙara da cewa shugaban Ƙasa ya yi alƙawarin ɗaukar ƙarin matakai domin shawo kan matsalar tsaro, yana mai cewa, “Ya jaddada cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi nan ba da jimawa ba.”

Zanga-zanga a Faɗin Jihohi

Duk da tattaunawar, ma’aikata sun fito kan tituna a Legas, Abuja, Anambra, Enugu, Borno, Gombe, Osun, Benue, Rivers, Ekiti, Abia, Imo da sauran jihohi, suna nuna damuwarsu kan yadda tsaro ya lalace.

A Abuja, ma’aikata sun taru a hedikwatar NLC, inda jami’an tsaro suka bazu domin tabbatar da zaman lafiya.

“Wannan zanga-zanga ce domin taimaka wa ƙasa – domin jan hankalin gwamnati kan illar rashin tsaro,” in ji Ajaero.

A Legas, zanga-zangar ta fara ne daga Ikeja Under Bridge zuwa Majalisar Dokokin Jihar Legas, inda shugabar NLC ta jihar, Funmi Sessi, ta ce yawan mahalarta ya nuna cewa ƴan Najeriya sun gaji.

“Mutane suna tsoron yin tafiya domin ziyartar ƴan uwansu saboda rashin tsaro,” in ji ta.

A wasu jihohi, shugabannin ƙwadago sun buƙaci sauya dabarun yaƙi da ta’addanci, gurfanar da ƴan bindiga da masu daukar nauyinsu, da kuma ƙarfafa tsarin tsaro.

A Sokoto kuwa, NLC ta zaɓi yin addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, bisa shawarar majalisar zartarwar jihar.

Rahoton Satar Mutane

TIMES HAUSA ta tattaro daga wani bincike na SB Morgen mai taken Economics of Nigeria’s Kidnapping Industry cewa, tsakanin Yunin 2024 da Yunin 2025, masu garkuwa da mutane sun buƙaci fiye da Naira biliyan 48, sai dai Naira biliyan 2.57 kacal aka biya su.

Rahoton ya nuna Arewa maso Yamma ce ta fi fuskantar matsalar garkuwa da mutane, yayin da Kudancin Kudu da Kudancin Gabas ke fama da sace-sacen da suka shafi kuɗi da rigimar addini.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

NLCZanga-Zanga
Comments (0)
Add Comment