NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama da iska a sassa daban-daban na Najeriya yau Lahadi

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta sanar da cewa ana sa ran samun ruwan sama mai ɗan yawa tare da guguwar iska a wasu yankunan Najeriya ranar Lahadi, 14 ga Satumba 2025.

Hukumar ta kuma gargaɗi mazauna yankunan da ke da hatsarin ambaliya da su kasance cikin shiri.

Rahoton da jami’an NiMet suka fitar ranar Asabar ya nuna cewa a Arewa, jihohin Kebbi, Sokoto, Zamfara, Kaduna, Kano, Katsina, Adamawa da Taraba za su fuskanci ruwan sama da iska a safiyar Lahadi.

Wakiliyarmu ta tattaro cewa daga baya da rana da kuma yammaci, ana sa ran samun guguwar iska da ruwan sama a Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Kaduna, Borno da Katsina.

A tsakiyar ƙasar, NiMet ta bayyana cewa za a sami gajimare tare da ɗan hasken rana da safe, amma da rana zuwa dare ana sa ran ruwan sama a yawancin jihohin yankin.

A kudu kuwa, jihohin Abia, Ebonyi, Delta, Akwa Ibom da Cross River za su fuskanci gajimare da yiwuwar samun ruwan sama da safe, sannan daga baya da rana zuwa dare ana sa ran samun ruwan sama a mafi yawan yankin.

NiMet ta gargaɗi cewa guguwar iska na iya janyo cikas ga wasu ayyukan waje.

Haka kuma ta shawarci direbobi da su yi taka-tsantsan yayin da ake ruwan sama saboda rage gani da kuma yanayin hanya mai haɗari.

Hukumar ta ƙara da cewa al’umman da ke zaune a wuraren da ake fama da ambaliya su kasance cikin shiri saboda yiwuwar aukuwar ambaliyar kwatsam.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

AmbaliyaNiMET
Comments (0)
Add Comment