Hukumar Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta sanar da cewa za a samu guguwar iska mai ƙarfi da ruwan sama a wasu sassan Najeriya a ranar Juma’a, 5 ga Satumba 2025, lamarin da ka iya haifar da jinkirin harkokin sufuri da wasu ayyukan waje.
Wakilinmu ya tattaro daga NiMet cewa jihohin Arewa kamar Taraba, Jigawa, Gombe, Bauchi, Kebbi, Sokoto, Zamfara, Kano, Kaduna da Katsina za su fuskanci guguwar iska da ruwan sama mai sauƙi da safe, yayin da da yamma zuwa dare za a samu ruwan sama mai yawa a Sokoto, Katsina, Kano, Zamfara, Kebbi, Kaduna, Taraba, Borno da Adamawa.
A yankin tsakiyar ƙasa kuma, ana hasashen samun ruwan sama mai sauƙi a Plateau da Benue da safe, sannan da yamma zuwa dare za a sami ruwan sama da guguwar iska a Nasarawa, Benue, Niger, Plateau, Kogi, Kwara da Babban Birnin Tarayya (FCT).
A Kudu, ana sa ran da asubar fari za a samu gajimare a Cross River, kafin a samu ruwan sama a lokutan yamma a Enugu, Ebonyi, Imo, Anambra, Abia, Edo, Delta, Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Bayelsa.
NiMet ta yi gargaɗi ga jama’a da su kasance masu lura.
“Iska mai ƙarfi na iya rage gani, ta sa hanyoyi su yi santsi, kuma ta hana ayyukan waje. Al’ummomi da ke zaune a wuraren da ruwa ke taruwa su kula,” in ji hukumar.