NiMet ta sanar da samun ruwan sama da iska mai ƙarfi a wasu sassan Najeriya a yau Asabar

Daga rahoton da wakilinmu ya tattaro daga Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta fitar, an bayyana yanda yanayin yini da daren yau Asabar, 6 ga Satumba, 2025 zai kasance.

A Arewa, NiMet ta bayyana cewa ana sa ran samun guguwar iska tare da ruwan sama mai sauƙi zuwa matsakaici da safe a wasu sassan Sokoto, Kebbi, Kaduna, Taraba da Adamawa.

Da rana kuma, an yi hasashen samun guguwar iska mai ɗauke da ruwan sama a Borno, Bauchi, Gombe, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kaduna, Taraba da Adamawa.

A Tsakiyar Najeriya kuma, ana sa ran samun guguwar iska da ruwan sama mai sauƙi a wasu yankunan Jihar Neja, Kwara, Nasarawa da Benue da safe, yayin da NiMet ta hango yiwuwar samuwar guguwar iska mai ruwan sama matsakaici a wasu sassan Nasarawa, Neja, Filato, Kogi, Kwara da babban birnin tarayya Abuja da yamma.

A Kudu, an yi hasashen samun gajimare da ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan Cross River da Akwa Ibom da safe, sannan ana sa ran samun ruwan sama na gajeren lokaci a mafi yawan sassan yankin da yamma.

NiMet ta gargaɗi mazauna yankunan da su yi hattara yayin da ake guguwar iska domin iska mai ƙarfi na iya kawo ƙarancin gani, kaucewa daga hanyoyi, da kuma iya katse harkokin waje.

Haka kuma, an shawarci mazauna yankunan da ke fama da ambaliya da su kasance cikin shirin kariya a duk lokacin da ruwan sama ya tsananta.

NiMET
Comments (0)
Add Comment