NiMet ta fitar da sabon gargaɗi kan yiyuwar samun ambaliya a jihohi 16

Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta sake fitar da sabon gargaɗi kan yiwuwar samun ambaliya, inda ta yi nuni da cewa jihohi 16 na fuskantar haɗarin ambaliya a kwanakin nan saboda yawan ruwan sama da kuma tsananin danshin ƙasa.

Wakilinmu ya tattaro daga sabuwar sanarwar NiMet cewa jihohi 16 da ke cikin babban haɗarin sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Borno, Adamawa, Niger, Oyo, Ogun, Lagos, Edo, Delta, Anambra, Akwa Ibom, Bayelsa, Rivers, da Cross River.

Sanarwar ta yi gargaɗin cewa irin wannan ambaliya na iya jawo mummunan yanayi ga al’umma, ciki har da tashin ƙananan ƙauyuka, lalata hanyoyin sufuri, gurɓata ruwan sha, lalata gonaki, tilasta wa al’umma yin ƙaura, da kuma ƙara haɗarin rasa rayuka da dukiyoyi.

“Ambaliya irin wannan ba wai gidaje da kasuwanci kaɗai take barazana wa ba, har ma da muhimman hanyoyin zirga-zirga da kuma aikin gona,” in ji NiMet, inda ta ƙara da cewa, “Al’umma na da muhimmiyar rawa wajen rage illar ta, don haka a ɗauki mataki tun yanzu.”

Hukumar ta bayar da shawarwari ga hukumomi daban-daban, inda ta shawarci gwamnatocin jihohi da hukumomin bayar da agajin gaggawa kamar NEMA da SEMA da su fara aiwatar da shirye-shiryen gaggawa, su baza sanarwar gargaɗi, su ƙara wayar da kan jama’a kan tsare-tsaren kare kai daga ambaliya, da kuma tanadar da kayan agaji a yankunan da ke cikin haɗarin.

Haka kuma an shawarci shugabannin ƙananan hukumomi da al’umma su share magudanan ruwa, su hana zub da shara a hanya, su kuma tsaurara matakan hana gine-gine a hanyoyin magudanan ruwa ko kusa da koguna.

An kuma shawarci jama’a su yi ƴar ƙwarya-ƙwaryar hijira zuwa wurare masu aminci idan an bayar da umarnin yin hakan.

A fannin noma, an shawarci manoma su girbe amfanin gonan da ya nuna kafin ruwan saman ya ƙara yawa, su yi amfani da dabarun sarrafa ruwa a gonakin da ke fuskantar ambaliya, su kuma kwashe shanu, sauran dabbobi, da kayan gona zuwa wurare masu tsaro.

An kuma gargaɗi jama’a da kada su riƙa ƙetare hanyoyin ruwa mai gudana, su kuma sanar da hukumomi duk wata alamar fara samun ambaliya a yankunansu.

NiMet ta jaddada cewa za ta ci gaba da bibiyar yanayin tare da fitar da sabbin rahotanni kan abin da ke faruwa, tana mai cewa: “Al’umma mai ilimi kan haɗari ita ce al’umma mai tsira. Sanin haɗari da ɗaukar mataki tun kafin faruwar abu na kare rayuka.”

NiMET
Comments (0)
Add Comment