Mutane 63 ne suka mutu, ciki har da sojoji, a sabon harin da Boko Haram ta kai Jihar Borno

Fushi da alhini sun mamaye Bama a Jihar Borno bayan aƙalla mutane 63, ciki har da sojoji biyar, sun rasa rayukansu a sabon harin da Boko Haram ta kai a garin Darajamal, wanda aka dawo da mazauna cikinsa kwanan nan bayan gudun hijirar shekaru.

Wakiliyarmu Fatima Abubakar Fullaty ta tattaro cewa maharan sun dirar wa al’umma ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a, inda suka buɗe wuta, suka ƙone gidaje, shaguna da motoci, kuma suka yi ta kashe jama’a na tsawon sa’o’i kafin agajin sojoji ya isa.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa, “An kashe sojoji biyar, amma na tabbata waɗanda aka kashe sun fi mutum 50. Sun yi ta aika-aika na tsawon lokaci kafin ƙarin wasu sojoji su iso.”

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, wanda ya ziyarci yankin a ranar Asabar, ya tabbatar da adadin waɗanda aka kashe, yana mai cewa, “Mutane 63 ne suka rasa rayukansu, ciki har da sojoji biyar. Wannan gari an dawo da shi ne kwanan nan, amma Boko Haram ta sake kawo masa hari.”

Ya kuma koka kan ƙarancin ma’aikatan tsaro a Najeriya, yana mai kira da a hanzarta tura sabbin jami’ai ƴan ƙato da gora na kare dazuka domin tallafawa rundunar sojoji wajen tsare al’umma masu rauni.

Rundunar Sojin Sama ta Ƙasa ta ce ta kashe fiye da ƴan Boko Haram 30 a mayar da martini kan harin, inda Air Commodore Ehimen Ejodame ya bayyana cewa jiragen yaƙi sun yi luguden wuta kan ƴan ta’addan da suka tsere daga Darajamal zuwa dazukan kusa.

Babban Jami’in Jin Ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Fall, ya la’anci harin, yana mai cewa, “Abin takaici ne sosai. Fararen hula bai taɓa kamata su zama manufar hari ba.”

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana wannan kisa a matsayin “ta’addanci na rashin hankali” kuma ya yi addu’ar samun rahamar Allah ga waɗanda suka rasu, tare da jaje ga iyalansu.

Sanata Ali Ndume da Sanata Kaka Shehu Lawan sun bayyana damuwarsu kan yawaitar hare-haren, suna kira ga Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da sabbin kayan aiki, fasaha da ƙarin ƙarfin rundunar tsaro.

Boko HaramBorno
Comments (0)
Add Comment