Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Aƙalla matasa takwas daga cikin sabbin ƴan kasuwa 80 a Jigawa waɗanda Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) ta horas sun samu tallafin naira miliyan biyu don inganta kasuwancinsu.
Ingantattun bayanai da PUNCH ta tattara daga CITAD sun nuna cewa shirin ya samu goyon bayan British Council da King’s Trust International, inda aka gudanar da horo na tsawon makwanni takwas a Cibiyar Bunƙasa Ma’aikata (MDI) Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Rahotanni sun ce rashin aikin yi da ƙarancin damar samun aiki na bisa doka sun ci gaba da kasancewa babbar barazana ga matasa a arewacin Najeriya.
A don haka, ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙara zuba jari a ɓangaren horaswa, jarin fara sana’a (seed funding), da kuma shirin jagoranci don tallafa wa matasa su zama masu dogaro da kansu.
Shugaban shirin daga British Council, Dr Yahya Janga, wanda shi ne Manajan Shirye-shiryen Ilimi na Wajen Makaranta – Matasa da Zaman Lafiya, ya yabawa gwamnatin Jigawa da Jami’ar Tarayya ta Dutse bisa tallafin da suka bayar.
Ya ce, “Jigawa ta bayar da cikakken goyon baya wajen ganin wannan shiri ya samu nasara. Muna kuma jinjinawa Jami’ar Tarayya ta Dutse bisa taimakonsu wajen zaɓar matasan da suka cancanta don wannan horo.”
Shi ma Daraktan CITAD, Malam Yunusa Zakariya’u, wanda mai gudanar da aikin, Malam Isa Garba, ya wakilta, ya bayyana cewa wannan aiki wani sashe ne na shirin Youth Connect na British Council.
Ya ce, “A Jigawa, mun horar da matasa 80 masu shekaru tsakanin 18 zuwa 30 daga faɗin jihar, inda guda takwas suka ci gajiyar tallafin bayan gasar gabatar da shirin kasuwanci (business plan). Wannan ci gaba ne wajen sauya bayar da horo zuwa ainihin bayar da damar yin kasuwanci, musamman a ɓangarorin fasahar zamani, ICT, kasuwanci, da ƙwarewa a hulɗa.”
Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Malam Sagir Musa, wanda mai taimaka masa, Abbas Zakari ya wakilta, ya gode wa masu shirya taron tare da jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da haɗa kai da ƙungiyoyin da ke da irin wannan hangen nesa.
Daga cikin masu cin gajiyar tallafin akwai Mohammed Bello, wani matashi mai naƙasa, wanda ya bayyana cewa zai yi amfani da kuɗin wajen bunƙasa sana’arsa.
Ya ce: “Ina kira ga matasa masu naƙasa su koyi sana’o’i, kada su dogara ga aikin ofis kaɗai. Haka kuma gwamnati ta samar da hanyoyin dogaro da kai gare mu.”
Haka itama wata matashiya mai suna Fiddausi Hamza, wadda ta ƙware a sana’ar epoxy resin, ta bayyana cewa tallafin zai taimaka mata ta maida horon da ta samu zuwa ainihin gudanar da kasuwanci.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook