Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Aƙalla mata 792 ne suka bar jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP) suka koma jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) a Jihar Jigawa.
Wakilinmu ya tattaro cewa matan sun bayyana sauyin sheƙarsu ne a wani taro da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, inda Uwargidar Gwamna, Hajiya Amina Umar Namadi, ta karɓe su a hukumance.
A jawabinta, Uwargidan Gwamna Namadi, ta bayyana wannan sauyin sheƙa a matsayin shaida ta kyakkyawan shugabanci da Gwamna Umar Namadi ke yi tare da jajircewarsa na inganta rayuwar jama’a, musamman mata da matasa.
Ta taya sabbin mambobin murna, inda ta kuma tabbatar musu da cewa, ƙofofin APC a buɗe suke ga duk wanda ke da niyyar shiga domin cigaban jihar.
Shi ma Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, wanda ya halarci taron, ya jaddada cewa wannan gwamnatin tana ƙoƙari wajen kawo ci gaba daga tushe.
Ya nuna cewa tun daga farkon mulkin, gwamnatin Namadi ta fito da manufofi da shirye-shirye da dama da nufin inganta walwalar jama’a.
A cewarsa, “Wannan gwamnati ta fi takwarorinta yin fice wajen isar da ribar demokaraɗiyya ga jama’arta.”
Da ta ke magana a madadin sabbin mambobin, Amina Waina, ta bayyana cewa dalilin da ya sa suka sauya sheƙa shi ne irin goyon bayan da gwamnati ke nunawa mata.
Ta yi alƙawarin cewa za su ci gaba da jan hankalin sauran mata don mara wa gwamnati baya a babban zaɓen 2027.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook