Majalissar Zartarwar Jigawa ta amince da ayyukan raya ƙasa na sama da naira biliyan 91 a zaman makonnan

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa, ta amince da aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da darajarsu ta kai ₦91,043,575,816.69, a zaman majalisar da aka gudanar a ranar 17 ga Disamba, 2025.

Matakan da aka ɗauka sun shafi ɓangarori masu muhimmanci da suka haɗa da wutar lantarki, hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi, muhalli, samar da ruwan sha, da bunƙasa fasaha.

TIMES HAUSA ta fahimci cewa waɗannan ƙudurori na nuni da ƙudurin gwamnatin jihar na ƙara haɓaka rayuwar al’umma, bunƙasa tattalin arziƙi, da tabbatar da ci gaban more rayuwa a faɗin ƙananan hukumomin jihar.

A cikin ƙudurorin, majalisar ta amince da bayar da kwangilar samar da lantarki da shigar da na’urorin hasken rana ga wasu hukumomin gwamnati da cibiyoyi a kan kuɗi ₦689,383,257.83.

Ayyukan sun haɗa da sayen taransifoma da samar ƙananan tashoshin lantarki a Jigawa State Polytechnic Dutse, GDSTC Gumel, Babura da Kafin Hausa, JTV, sansanin horaswa na NYSC, filin wasan Dutse wato Township Stadium, asibitocin ƙwararru a Hadejia da Kazaure, asibitocin Ringim, Birnin Kudu da Bulangu, Khadija University, Bamaina Academy, kasuwannin Sara, Gujungu da Maigatari, da kuma Polytechnic of Communication and Information Technology, Kazaure.

Haka kuma, majalissar ta amince da gina cibiyoyin horaswa da sauya motoci zuwa amfani da iskar gas (CNG) a Dutse da Hadejia, a kan kuɗi ₦563,003,475.71, inda Dutse ta samu ₦214,145,586.71, yayin da Hadejia ta samu ₦348,857,889.00.

A wani muhimmin mataki na samar da makamashi mai ɗorewa, majalisar ta amince da gina ƙananan tashoshin wutar lantarki masu amfani da hasken rana (solar mini-grids) a Fadar Gwamnati, Ofishin Mataimakin Gwamna, gidajen SSG da HOS, Sakatariyar Jiha, Majalisar Dokoki, Ɓangaren Shari’a da tashar ruwan Shuwarin/Gidan Ihu, a kan kuɗi ₦15,242,401,992.00.

Majalisar ta kuma amince da sake fasalin kasafin kuɗi, inda aka mayar da ₦4.5 biliyan daga Asusun Raya Kasuwanni da ₦1.0 biliyan daga Asusun Tabbatar da Daidaito zuwa Ma’aikatar Ayyuka, domin biyan kuɗin fara gina hanyoyin cikin birane.

Ɗaya daga cikin manyan ayyukan shi ne gina hanyoyin cikin birane masu tsawon kilomita 58.56, da suka haɗa da Dutse Phase II (20.36km), Kafin Hausa (19km), Gumel Bypass (12km), Dangyatim (4.2km) da Doko a Ƙaramar Hukumar Garki (4km), a kan kuɗi ₦57,798,380,827.20.

A ɓangaren addini, majalisar ta amince da gina masallatai a GDTQ Yusuf Dantanoma, Yalleman (Kaugama), Fadawa, Sarawa (Kafin Hausa) da Rigar Liman (Maigatari), ta hannun Hukumar Ilimin Musulunci, a kan kuɗi ₦204,027,847.50.

Majalissar ta kuma amince da gina Cibiyar Binciken Ƙasar Noman Rani a Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, a kan kuɗi ₦557,081,291.25, da kuma gina ɗakunan kwanan ɗalibai da gidajen ma’aikata a Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Limawa, Dutse, a kan kuɗi ₦1,070,345,133.90.

Haka zalika, an amince da gyarawa da sabunta Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Ringim a kan kuɗi ₦506,577,401.40.

A fannin kiwon lafiya, majalisar ta amince da gyarawa, sabuntawa, da sanya kayan aiki ga manyan asibitoci da dama, ciki har da Hadejia, Gumel, Kazaure da Birniwa; gyaran Asibitin Mahaukata na Kazaure; inganta asibitocin Gwiwa, Garki, Guri, Gantsa, Gagarawa da Kirikasamma; samar da kayan aikin Asibitin Ƙashi na Gumel; da na’urorin wankin ƙoda ga asibitocin Dutse, Ringim da Kazaure, a kan kuɗi ₦8,051,282,260.58.

Domin daƙile barazanar ambaliyar ruwa, majalissar ta amince da gina magudanan ruwa a Tumballe da Garun Gabas (Mallam Madori), Kila, Farin Dutse da Asibitin Gwaram, Maigatari, Kafin Hausa, da Kwalejin Ilimi ta Gumel, a kan kuɗi ₦4,885,603,497.79.

A ƙoƙarin ci gaba da riƙe matsayin Jigawa a matsayin Jihar da ba ta yin bahaya a fili (ODF), majalisar ta amince da gina gidajen biyan buƙata na jama’a a kasuwannin Kubsa, Sara da Babura, a kan kuɗi ₦359,250,552.00.

Majalisar ta kuma amince da sayen kayan aiki domin shirin Jigawa Tech Talent Acquisition Programme, a kan kuɗi ₦210,246,845.00, domin bunƙasa haziƙan matasa a ɓangaren ICT.

Haka nan, an amince da sayen motoci – Toyota Corolla, bas mai kujeru 18 da Hilux – domin Hukumar Ilimin Sakandare ta Jiha, a kan kuɗi ₦329,111,250.00.

Sauran ƙudurorin sun haɗa da gina magudanan ruwa a Kiyawa domin kula da ruwan sama, a kan kuɗi ₦576,880,184.54, da kuma amincewa da sabuwar Dokar Kare Lafiyar Abinci da Ƙa’idojinta, kamar yadda kwamitin da majalissar ta kafa ya gabatar, bisa shawarar Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi.

TIMES HAUSA ta fahimci cewa waɗannan ƙudurori na nuna cikakken tsari da hangen nesa na gwamnatin Jigawa wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa, inganta rayuwar al’umma, da ƙarfafa gina tattalin arziƙin jihar baki ɗaya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Gwamna NamadiJigawa
Comments (0)
Add Comment