Majalisar Sarakunan Idoma ta bayyana cewa ta soke sarautar gargajiya da aka bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da wasu mutane huɗu a lokacin bikin Igede Agba a Ƙaramar Hukumar Oju, Jihar Benue.
Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin cewa wannan sarauta, wacce Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya karɓa a madadin Shugaban Ƙasa daga hannun Adiharu na Igede, Mai Martaba CP Oga Ero (mai ritaya), a ranar Asabar, ta saɓawa umarnin da Majalisar Idoma ta bayar tun farko na dakatar da bayar da sarautun gargajiya a faɗin ƙasar Idoma.
Sanarwar, wacce Sakataren Majalisar, Mista Adegbe Uloko, ya sanya wa hannu, kuma mai taken “Soke Sarautun Da Aka Bayar Ta Igede Traditional Council,” ta ce duk irin waɗannan naɗin sarauta ba su da inganci a doka ko gargajiya, don haka babu su, babu kuma abin da za a ɗauke su da shi.
Majalisar ta jaddada cewa ita ce kawai hukuma ta gargajiya da gwamnati ta amince da ita a yankin Idoma, kuma duk wani aiki da ya saɓawa umarninta ya saɓawa doka.
“Wannan sanarwar an yi ta ne domin kare mutuncin al’adun gargajiya a Jihar Benue, tabbatar da bin ƙa’ida, da kiyaye zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Idoma,” in ji sanarwar.
Majalisar ta kuma buƙaci jama’a, hukumomin gwamnati, da masu ruwa da tsaki na gargajiya su yi watsi da sarautun da aka bayar ga Shugaban Ƙasa Tinubu da sauran waɗanda aka karrama.