Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Kungiyar Likitoci masu Neman Ƙwarewa ta Ƙasa (NARD) ta fara yajin aikin gargaɗi na tsawon kwanaki biyar, duk da tabbacin da gwamnatin tarayya ta bayar na cewa za a iya kaucewa hakan.
Yajin aikin ya fara ne da misalin ƙarfe 8 na safe a ranar Juma’a, 12 ga Satumba 2025, kuma zai ƙare a ranar Talata, 16 ga Satumba.
Wannan na zuwa ne bayan ƙarewar wa’adin sa’o’i 24 da suka bai wa gwamnati domin warware buƙatunsu, bayan wani wa’adin kwanaki 10 da ya ƙare a ranar 10 ga Satumba ba tare da mafita ba.
Wakilinmu ya fahimci cewa waɗannan likitoci su ne likitocin da suka kammala makarantar likitanci amma ke ƙara samun ƙwarewa a wasu fannoni.
Su ne suka fi rinjaye a ɗakunan bayar da agajin gaggawa na asibitoci a Najeriya, lamarin da ke sanya gudunmawarsu ta zama muhimmiya a harkar lafiya.
A cikin wata sanarwa mai taken “Ayyana Yajin Aiki” da Sakatare Janar na NARD, Dr Oluwasola Odunbaku, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta tabbatar da cewa yajin aikin ya kankama.
A cewarsa: “Kamar yadda muka bayyana a sanarwarmu ta baya, yajin aikin ya fara ne da ƙarfe 8:00 na safe yau (jiya) Juma’a. Dukkan shugabannin cibiyoyi su tabbatar sun jagoranci mambobinsu yadda ya dace.”
Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da NARD ta fitar a ranar 1 ga Satumba 2025, wadda Shugaban ƙungiyar, Dr Osundara, tare da Dr Odunbaku da kuma Sakataren Yaɗa Labarai, Dr Omoha Amobi, suka sanya wa hannu, cewa buƙatun likitocin sun haɗa da:
- Biyan kuɗin Medical Residency Training Fund na shekarar 2025 da ake bi bashi.
- Biyan bashin watanni biyar daga ƙarin albashin CONMESS da aka amince da shi kashi 25–35 cikin 100.
- Warware sauran bashin albashi da su ke bi.
- Biyan kuɗin kayan aiki (accoutrement allowance) na shekarar 2024.
- Sakin kuɗin alawus na ƙwararru cikin gaggawa.
- Mayar da matsayin takardar shaidar membobinsu zuwa West African Postgraduate Medical College.
Sun kuma buƙaci Kwalejin Koyar da Likitanci ta Ƙasa (NPMCN) da ta bayar da takardun shaidar memba ga duk wanda ya cancanta, tare da aiwatar da ƙarin albashin 2024 (CONMESS), da warware matsalolin walwalar likitoci a Jihar Kaduna, da kuma magance matsalolin da likitocin ke fuskanta a asibitin koyarwa na LAUTECH da ke Ogbomoso.
Sai dai a wani martani da ya yi kafin yajin aikin, Ƙaramin Ministan Lafiya, Dr Isaq Salako, ya bayyana fatan cewa tattaunawa da ƙungiyar NARD za ta kai ga kaucewa yajin aikin.
A cewarsa: “Ƙungiyar likitocin ta fitar da wa’adin ƙarshe, amma ina ganin da irin tattaunawar da ake yi yanzu, muna samun ci gaba.”
Ya bayyana cewa babbar matsalar ita ce biyan alawus na koyar da likitoci, inda ya bayyana cewa har yanzu gwamnati ba ta biya kusan kashi 40 cikin 100 na kuɗaɗen shekarar 2025 ba.
“Fatanmu shi ne kafin wa’adin ya ƙare, za a iya magance matsalar,” in ji shi.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook