Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Ƙungiyar Nigerian Association of Resident Doctors (NARD) ta bayyana takaici kan rashin daidaituwar adadin likitoci da marasa lafiya a Najeriya, inda kowane likita ɗaya ke kula da mutane 9,083 – lamarin da suka ce ya yi nisa da ƙa’idar duniya.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar 1 ga Oktoba, 2025, domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ƴancin kai, ƙungiyar ta sanar da cewa daga yau, dukkan likitocin ƙungiyar ba za su ƙara yarda da yin aiki mai tsawon fiye da awanni 24 ba a jere, domin kare kansu daga gajiya mai barazana ga rayuwarsu.
Sanarwar, wacce shugaban NARD, Dr. Mohammad Suleiman, da Babban Sakatare, Dr. Shuaibu Ibrahim, tare da jami’in yaɗa labarai, Dr. Abdulmajid Ibrahim, suka sanya wa hannu, ta ce Najeriya na da likitoci masu aiki ƴan ƙungiyar kusan 11,000 kacal, duk da yawan jama’a sama da miliyan 240 a Najeriya.
Wakilinmu ya tattaro cewa, Ministan Lafiya, Prof. Muhammad Pate, ya tabbatar da cewa likitoci sama da 16,000 sun bar ƙasar cikin shekaru bakwai da suka wuce domin neman aikin da ya fi biyan buƙatunsu a ƙasashen waje.
Wannan ya sa ƴan kaɗan da suka rage ke ɗaukar nauyin aikin asibitoci, musamman ma a manyan asibitoci.
Ƙungiyar ta bayyana cewa, “Likitocin Najeriya suna aiki awanni 106.5 a mako, yayin da masu tiyata ke aiki sama da awanni 122.7 a mako, wanda ya yi daidai da yin kiran gaggawa har sau biyar a mako. Wannan yanayi ba wai kawai yana cutar da marasa lafiya ba, har ma yana barazana ga lafiyar likitocin kansu.”
NARD ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta kafa tsarin musanya na likitoci ɗaya-da-ɗaya domin rage nauyi, tare da kafa dokokin kariya da za su taƙaita tsawon lokacin aiki.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa likitocin da suka ci gaba da zama a Najeriya duk da wahalhalu “jarumai ne da suka cancanci samun kariya da ingantaccen albashi.”
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook