Kamfanin Sufuri na Jihar Gombe, wanda aka fi sani da Gombe Line, ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da bai wa matafiya tsari mai sauƙi da araha a duk manyan hanyoyin Najeriya.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da wakilyarmu Fatima Abubakar Fullaty ta samu daga kamfanin a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025, wadda Shugaban Sashen Sadarwar a Kafafen Sadarwa na Zamani na kamfanin, Muhammad Sani Usman, ya sa wa hannu.
“Mun ɗauki nauyin ci gaba da yi muku hidima da mafi ƙarancin kuɗin mota tare da samar da mafi kyawun jin daɗin tafiya,” in ji shi.
Sabbin farashin da kamfanin ya bayyana sun haɗa da tafiya daga Gombe zuwa Abuja ko Kaduna a kan ₦15,000, zuwa Legas a kan ₦30,000, zuwa Fatakwal ₦25,000, zuwa Kano ₦8,500, da zuwa Bauchi ₦4,000.
Sauran sun haɗa da Gombe zuwa Katsina ₦12,000, Makurdi ₦16,000, Jos ₦7,500, Lafiya ₦13,000, Maiduguri ₦9,500, Damaturu ₦6,000, Potiskum ₦5,000, Minna ₦16,000, Sokoto ₦19,000, Zamfara ₦15,000, Yola ₦6,500, Jalingo ₦8,000, Gusau ₦16,000, Zaria ₦12,000, Azare ₦4,500, Biu ₦3,500, Billiri ₦1,200, da Kaltungo a kan ₦1,400.
Kamfanin ya yi kira ga matafiya da su ci gaba da tafiya cikin nutsuwa da aminci tare da Gombe Line, yana mai tabbatar da cewa tsaro, kwanciyar hankali da gamsuwar matafiya su ne ginshiƙan ayyukansa.