Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnatin Jihar Jigawa ta karrama wasu malamai na makarantun kimiyya da fasaha da suka yi fice a shekarar 2025.
An raba lambobin yabo da kyaututtuka na kuɗi domin nuna yabawa ga jajircewa da ƙwarewar da suka nuna.
Gwamna Umar Namadi ya ce wannan tsari na ƙarfafa gwiwar malamai zai taimaka wajen inganta ilimi a faɗin jihar.
“Idan ana hukunta mai laifi, ya kamata a karrama mai ƙwazo,” in ji shi.
Shi ma Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha, Farfesa Abbas Badakaya, ya ce an yi amfani da ƙa’idoji na musamman wajen zaɓar waɗannan malamai, ciki har da jajircewa, bin ƙa’idojin lokaci da nuna ƙwarewa.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook