Jigawa ta bai wa Ƴan Sanda gudunmawar motocin sintiri 10 don ƙarfafa tsaro

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta bayyana godiyarta ga Gwamna Malam Umar Namadi, bisa kyautar motoci 10 ƙirar Toyota Hilux da gwamnatin jihar ta bai wa rundunar don ƙarfafa aikin tsaro.

TIMES HAUSA ta tattaro cewa bikin miƙa motocin ya gudana ne a ofishin sakataren gwamnatin jihar a Dutse ranar Juma’a, 31 ga Oktoba, inda aka miƙa motocin ga kwamishinan ƴan sanda, CP Dahiru Muhammad.

Wannan kyauta, a cewar rundunar, na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen tallafawa hukumomin tsaro don kare rayuka da dukiyoyi.

Kwamishinan ƴan sanda ya yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan taimako, yana mai cewa motocin za su taimaka wajen inganta saurin amsa kiran gaggawa da kuma tabbatar da tsaro a sassan jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa za a yi amfani da motocin yadda ya kamata tare da kula da su domin ɗorewar amfaninsu.

Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro da al’umma domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

A ƙarshen sanarwar, kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya buƙaci jama’a da su kasance masu bin doka da bayar da haɗin kai wajen samar da tsaro ga kowa da kowa.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Jigawa
Comments (0)
Add Comment