Iyaye a Jigawa sun koka kan tsadar kayan makaranta yayin da ake shirin komawa karatu

Rahoton da jaridar PUNCH ta tattara a Dutse, Jihar Jigawa, ya nuna cewa iyaye a jihar na kokawa kan hauhawar farashin kayan makaranta yayin da makarantun gwamnati da na kuɗi ke shirin komawa karatu a ranar Litinin mai zuwa don fara sabon zangon karatu.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta Mai Zurfi ta jihar ta fitar, wacce ta tabbatar da shirin komawa aji ga malamai da ɗalibai da kuma kammaluwar dukkan shirye-shirye.

A tattaunawa daban-daban da iyaye suka yi da wakilin jaridar, sun bayyana cewa matsin tattalin arziƙi na ƙara tsananta musu wajen tanadar abubuwan da ake buƙata.

Hauwa Bello, wata uwa mai yara uku, ta ce, “Sanya yara makaranta na nufin samar musu sababbin kaya, littattafai, da kuɗin makaranta, wanda ya yi mana tsada matuƙa.”

Wani uba, Musa Aliyu, wanda ƴaƴansa ke karatu a makarantar sakandare ta kuɗi, ya ce, “Yawancin iyalai suna fama da biyan buƙatun yau da kullum, yanzu kuma an ƙara kuɗin makaranta a kai.”

Iyaye da ke da ƴaƴa a makarantun gwamnati, ciki har da Malam Usman Sani da Fatima Yusuf, sun bayyana irin wannan damuwa amma sun nuna ƙwaring gwiwar samun mafita.

“Ko makarantar gwamnati ce, sai an sayi littattafan rubutu da uniform, wanda duk kuɗi ne. Muna roƙon Allah ya inganta mana rayuwa,” in ji Malam Usman.

Wata bazawara mai yara uku, Fatima Yusuf, ta bayyana cewa tsadar rayuwa ta rage ƙarfin kuɗinta, tana mai cewa tsadar ilimi ta zama babbar matsala ga iyalai da dama a Jigawa.

A halin da ake ciki, malamai a jihar sun bayyana shirye-shiryensu na komawa aji, inda Saudatu Yusuf, malamar makarantar sakandare ta ƴan mata a Dutse, ta ce, “Muna dab da kammala shirye-shirye. Mun gama rubuta darussanmu, mun kuma tabbatar da cewa kayan koyarwa suna nan.”

Sai dai wani malami a makarantar firamare ta Dundubus, Saminu Shehu, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta gyara ajujuwan da suka lalace.

“Duk da cewa muna sa ran komawa, muna cikin damuwa da halin wasu ajujuwa. Muna fatan ma’aikatar za ta magance wannan matsalar nan kusa,” in ji shi.

A baya bayan nan dai wasu gwamnatocin jihohi a Najeriya sun fitar da tsarin sauƙaƙawa iyayen wajen hana bukukuwan kammala karatun firamare da sikandire, da kuma samar da tsarin mai sauƙi na mallakar kayan karatu, lamarin da wasu iyayen a Jigawa ke fatan jihar ta ɗabbaƙa domin a samu sauƙi.

Jigawa
Comments (0)
Add Comment