INEC ta amince da sabon shugabancin jam’iyyar ADC na ƙasa

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da sabon shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), lamarin da ya samu yabo daga ƴan jam’iyyar da kuma magoya bayan demokaraɗiyya a Najeriya.

Wakilinmu ya tattaro cewa tsohon Ministan Wasanni, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Muna taya mambobin ADC da duk masu kishin demokaraɗiyya a Najeriya murna. Muna yaba wa hukumar INEC da shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu, saboda tsaya wa a kan gaskiya da kuma kare demokaraɗiyya mai tsarin jam’iyyu da dama.”

Haka zalika, ƙungiyar ADC Vanguard ta bayyana a shafinta cewa, “Yanzu ya zama doka! INEC ta amince da sabon shugabancin ADC. Wannan tarihi ne da aka rubuta sakamakon jajircewar shugabanninmu da haɗin kan masu neman sabuwar Najeriya.”

Sun kuma yi ƙarin bayani da miƙa gaisuwar musamman ga wasu manyan ƴan siyasa ciki har da Nasir El-Rufai, Chibuike Amaechi, Atiku Abubakar, Peter Obi, Aminu Waziri Tambuwal, Rauf Aregbesola, da Bolaji Abdullahi.

A wani rubutun da ya shafi wannan, shugaban matasan jam’iyyar ADC na ƙasa, Balarabe Rufa’i, ya bayyana cewa, “INEC ta tabbatar da David Mark da sauran manyan mambobi a matsayin shugabannin jam’iyyar ADC. Wannan ya nuna cewa ADC jam’iyyar talakawa ce, ba ta masu cin amana ba. Lokacin kafa sabon adalci da gaskiya ya zo.”

ADCINEC
Comments (0)
Add Comment