ICPC ta nemi a sake fasalin yaƙi da cin hanci a jihohi da ƙananan hukumomi

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Sauran Laifuka Masu Alaƙa da Shi a Ma’aikataun Gwamnati (ICPC), Dr. Musa Adamu Aliyu, SAN, ya yi kira da a sake dubawa tare da sabunta tsare-tsaren yaƙi da cin hanci da rashawa a matakan jihohi da ƙananan hukumomi, domin rufe giɓin shugabanci da ake amfani da shi wajen sace dukiyar al’umma.

Kakakin ICPC, Mista Okor Odey, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.

A cewarsa, Dr. Aliyu ya yi wannan kira ne yayin zama na 11 na Taron Ƙasashen da suka rattaba hannu kan Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (UNCAC), wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar.

Shugaban ICPC ya bayyana cewa sake fasalin waɗannan tsare-tsare zai taimaka wajen magance ramuka a tsarin mulki da ake amfani da su sakamakon raunin hanyoyin sa ido, musamman a matakan da suka fi kusanci da rayuwar talakawa.

Shugaban, wanda Babban Lauya ne a Najeriya (SAN), ya jaddada cewa dole ne a tunkari cin hanci da rashawa a inda dukiyar jama’a da ayyukan gwamnati ke haɗuwa kai tsaye da ƴan kasa.

Ya yi tabbatar da cewa mayar da hankali kan yaƙi da cin hanci a matakin tarayya kaɗai na iya magance manyan giɓi a ƙananan hukumomi, inda tsare-tsaren hukuma da kulawar jama’a ke da rauni.

Ya ce, “Najeriya na da ƙananan hukumomi 774, kuma ICPC ba ta da isassun ma’aikata da za su ba ta damar kasancewa a kowace ƙaramar hukuma.”

A cewarsa, wannan ne ya sa aka fi karkata zuwa dabarun rigakafi, ciki har da tantance haɗarin cin hanci tun kafin ya faru.

Shugaban hukumar ya yi nuni da ginshiƙai takwas na tantancewa da Cibiyar Bayyanar Kasafin Kuɗi da Mutuncin Jama’a (Centre for Fiscal Transparency and Public Integrity) ta ƙirƙira, yana mai bayyana su a matsayin kayan aiki masu muhimmanci wajen ƙarfafa tsarin shugabanci a matakin ƙasa.

Hakazalika, Dr. Musa ya jaddada muhimmancin shigar da ƴan kasa cikin yaƙi da cin hanci a matakin tushe.

Ya bayyana cewa wannan ne ya haifar da ƙaddamar da shirin Accountability and Corruption Prevention Programme in Local Government Areas (ACPP-LG) a watan Afrilun 2025.

Ya ce, “An tsara wannan shiri ne domin daƙile cin hanci da laifuka masu alaƙa da shi a matakin ƙananan hukumomi ta hanyar ƙarfafa al’umma, zurfafa gaskiya da riƙon amana, da kuma ƙarfafa hanyoyin bayar da rahoto da ƙorafe-ƙorafe.”

Shugaban ICPC ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da su kafa tsare-tsaren gaskiya na dindindin, su ƙarfafa hanyoyin kula da kuɗaɗen gwamnati, tare da daidaita tsarin saye da sayarwa da ƙa’idojin duniya na riƙon amana.

Ya buƙaci ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, hukumomin sa ido, da ƙungiyoyin farar hula, domin cimma nasara a yaƙi da cin hanci da rashawa.

Dr. Musa Adamu Aliyu ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar barazana mai tsanani ta zirarewar kuɗaɗen shiga da gurɓacewar aiwatar da ayyuka, sakamakon rashin bayyana kasafin kuɗi, hauhawar da farashin kwangiloli, almundahanar albashi ta hanyar ma’aikatan bogi, da raunin hanyoyin binciken kuɗi a matakan jihohi da ƙananan hukumomi.

A ƙarshe, ya jaddada cewa domin cimma ci gaba mai ɗorewa da rage talauci, dole ne bin ƙa’idojin yaƙi da cin hanci su zama wani ɓangare na al’adun gudanarwa a jihohi da ƙananan hukumomi baki ɗaya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

ICPC
Comments (0)
Add Comment