Hukumar Kula da Ilimin Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NMCN) ta sanar da soke doguwar dokar da ta daɗe tana tilasta wa ɗaliban koyon aikin jinya da suka kasa haye jarabawar ƙwararru har sau uku su bar makaranta.
Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da aka rarraba ranar 1 ga Satumba, 2025, wacce Shugaban Hukumar kuma Babban Sakatarenta, Ndagi Alhassan, ya sanya wa hannu, cewa daga yanzu duk ɗaliban da suka faɗi wani sashe na jarabawar za su iya sake rubuta sashen har sai sun samu nasara, muddin sun cika aƙalla kashi 80 cikin 100 na halartar darussa da horo a asibitoci.
A cewar sanarwar, wacce ke ɗauke da taken “Sauye-Sauye a Ilimin Jinya: Soke Dokar Kora Bayan Kasa Cin Jarabawa Sau Uku,” wannan gyara na nufin ƙirƙirar yanayin koyo mai faɗi, sauƙi, da tallafi, tare da bin tsarin sauran sassan duniya.
“Daga wannan lokaci, wannan doka ta korar ɗalibi daga karatu bayan faɗuwa jarabawar ƙwararru sau uku a hukumar ta zo ƙarshe,” in ji sanarwar.
Hukumar ta kuma yi gargaɗi ga cibiyoyin koyar da ilimin aikin jinya da su tabbatar da ɗalibai suna cika ƙa’idojin zuwa aji kafin a sake ba su damar sake rubuta jarabawar, tare da sanar da cewa duk wani ƙoƙarin sake rubuta jarabawar da bai yi nasara ba zai shiga cikin alhakin makarantar da ta horar da ɗalibi.
NMCN ta jaddada cewa manufarta ita ce “ƙarfafa inganci da ƙwarewa a ilimi da aikace-aikacen jinya da ungozoma” ta hanyar samar da sauye-sauyen da suka mayar da hankali kan ɗalibai da kuma ci gaba da koyo na tsawon rai.
Sanarwar ta yi kira ga shugabannin makarantu da masu shi su samar da hanyoyin tallafawa ɗalibai, musamman waɗanda ke buƙatar ƙarin lokaci da taimako don ƙara basira, tare da tabbatar da cewa sauye-sauyen sun isa ga ma’aikata da ɗalibai domin cika burin NMCN na haɓaka ilimi bisa ƙa’idojin ƙasa da na duniya.