HASASHEN YANAYI: NiMet ta fitar da gargaɗi kan samun ruwan sama da yiwuwar ambaliya a jihohi biyar

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Asabar, 13 ga Satumba, 2025, inda ta yi gargaɗin samun ruwan sama mai ɗauke da guguwa a sassa daban-daban na ƙasar.

A cewar hukumar, da safe ana sa ran samun ruwan sama a jihohin Katsina, Kano, Adamawa, Gombe, Bauchi, Borno da Taraba.

Da yammaci kuma, rahoton ya nuna yiwuwar ruwan sama a Borno, Adamawa, Taraba, Gombe, Bauchi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa da Kebbi.

A yankin tsakiyar Najeriya kuwa, akwai yiwuwar samun ruwan sama a Abuja, Benue, Nasarawa da Neja da safe, sannan daga bisani a ci gaba da samun ruwan sama a Neja, Nasarawa, Filato, Kwara, Kogi, Benue da babban birnin tarayya Abuja.

Ga kudancin ƙasar kuma, hasashen ya nuna yiwuwar samun ruwan sama matsakaici a Ogun, Ondo, Oyo, Edo, Delta, Legas, Ribas, Cross River da Akwa Ibom da safe.

Daga baya kuma ana sa ran samun ruwan sama mai yawa a Imo, Abia, Enugu, Anambra, Ebonyi, Oyo, Ondo, Osun, Ogun, Ekiti, Legas, Edo, Delta, Ribas, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom.

NiMet ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya musamman a Delta, Legas, Ribas, Akwa Ibom da Cross River, tare da shawartar jama’a a yankunan da ke da rauni da su kasance cikin shiri.

Haka kuma, ta roƙi direbobi da masu tafiya su yi taka-tsantsan yayin da guguwar iska ke tasowa da ruwan sama don guje wa haɗari.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

NiMET
Comments (0)
Add Comment