Hasashen samun ruwan sama a sassan Najeriya na yau Alhamis daga NiMet

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta bayyana cewa za a samu ruwan sama mai tafe da guguwar iska a wasu sassan ƙasar a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.

Wannan hasashen na daga cikin sanarwar yau da kullum da hukumar ta fitar a daren jiya Laraba.

Wakiliyarmu ta gano daga sanarwar cewa, a yankin Arewa, za a samu yanayi mai hadari da hasken rana da safe, kafin daga bisani da yamma a samu ruwan sama da guguwar iska a jihohin Kaduna, Kebbi, Kano, Katsina, Zamfara, Adamawa da Taraba.

A tsakiyar Najeriya kuma, yanayin irin wannan na gajimare da ruwan sama zai shafi Abuja da Kogi, Benue, Kwara da Niger.

A kudancin Najeriya, NiMet ta ce tun da safe za a samu ruwan sama tare da guguwar iska a jihohin Ekiti, Ebonyi, Anambra, Enugu, Akwa Ibom da Cross River, yayin da a yammacin ranar za a samu ƙaruwar ruwan tare da guguwar iska a mafi yawan sassan yankin.

Hukumar ta yi gargaɗi cewa irin wannan yanayi na iya jawo tsaikon ayyukan waje, rage ganin hanya ga masu tuƙi, da kuma yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wuraren da ke da rauni.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

AmbaliyaNiMET
Comments (0)
Add Comment