Haɗarin mota ya yi tonon silili, NDLEA ta kama tabar wiwi kilogiram 112 bayan motoci 2 sun yi karo

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Kano ta ce ta gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 112, bayan haɗarin mota da ya rutsa da wata Golf da ta yi karo da babbar mota a kan hanyar Zaria–Kano, a Gadar Tamburawa.

Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar kakakin hukumar a Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari, wanda ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Asabar, 6 ga Satumba 2025.

A cewarsa, jami’an NDLEA da ke sintiri sun garzaya wurin haɗarin domin ceto direba da fasinjan motar Golf.

Amma fasinjan ya yi yunƙurin tserewa bayan an buɗe kofar motar, sai dai jami’an da ke wajen sun cafke shi.

Binciken da aka gudanar ya kai ga gano buhuna uku ɗauke da tabar wiwi da kuma kwalaye 150 na ƙwaya, jimillar nauyinsu ya kai kilogiram 112.

Rahoton ya ce direban, wanda yanzu haka yana samun kulawar likita, ya amsa cewa shi ne wakilin mai kayan, kuma ya sha yin irin waɗannan jigilar a baya a Kano da wasu jihohi.

Kakakin NDLEA ya tabbatar da cewa waɗanda aka kama za su fuskanci shari’a, tare da godewa jami’an da suka nuna ƙwarewa da hanzari wajen ceto rayuka da kuma gano miyagun ƙwayoyin.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su guji safarar ƙwayoyi, tare da riƙa bayar da bayanai game da duk wani motsi da ya shafi fataucin miyagun ƙwayoyi.

NDLEA
Comments (0)
Add Comment