Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi, ta amince da aiwatar da wasu muhimman ayyuka da suka shafi ilimi, noma, makamashi, da kuma tsarin kuɗi a zaman da ta gudanar ranar Litinin 22 ga Satumba, 2025.
Rahoton wakilinmu ya tattaro cewa, cikin matakan da aka ɗauka akwai amincewa da ₦869,638,271.18 don gyaran ginin wasu makarantun tsangaya guda 7, da kuma gina ɗakunan karatun Alƙur’ani 30 tare da filayen karatu 30 a kowace mazaɓa ta jihar.
Wannan zai bai wa ɗalibai almajirai damar samun ingantaccen muhalli na ilimi da kuma haɗa tsarin tsangaya da ci gaban ɗan adam a jihar.
Haka kuma, Majalisar ta amince da biyan ₦1,547,614,974.00 ga ɗalibai 22,388 ƴan asalin Jigawa da ke karatu a jami’o’i da kwalejoji guda 83 a cikin gida da waje.
Wannan tallafin kuɗin karatu ya haɗa da maza 13,622 da mata 8,766, don rage nauyin iyaye da kuma ƙarfafar ɗalibai don su cimma nasarar karatun da suke.
A ɓangaren noma, gwamnati ta amince da sakin ₦396,000,000.00 don biyan bashin takin da aka karɓa daga Gwamnatin Tarayya.
An ware wa Jigawa tireloli 20 na taki NPK (buhu 12,000) a farashin tallafi na ₦33,000 kan kowane buhu domin tallafa wa ƙananan manoma a shirin damina na 2025/2026.
Haka zalika, an amince da shirin TVET (Technical and Vocational Education and Training) a manyan cibiyoyi 21 a Jigawa, wanda zai ci ₦835,008,875.00.
Shirin zai ƙunshi cibiyoyin ƙwarewa guda 4, manyan makarantun kimiyya 6, cibiyoyin koyon sana’o’i 7 da kuma kwalejojin gwamnati guda 4, domin ba matasa ƙwarewar sana’o’in zamani.
Majalisar ta kuma amince da buɗe sababbin bankunan Microfinance guda 5 a Birniwa, Gujungu-Taura, Guri, Gwaram da Kaugama domin bunƙasa haɗin kai a harkokin kuɗi da kuma inganta ƙananan sana’o’i.
Bugu da ƙari, an ba da kwangilar ₦733,122,187.23 don gudanar da bincike da tsare-tsare na samar da solar ta saman rufi a makarantu, cibiyoyin lafiya da muhimman wuraren jama’a.
Wannan dai ya dace da manufar gwamnati na amfani da makamashi mai tsafta da rage dogaro ga wutar lantarki a ƙasa.
A fannin ilimi kuma, gwamnati ta amince da kashe ₦779,269,895.00 don samar da litattafai 68,850, fararen allunan aji 700, kwalayen marker 3,000 da kuma babura 295 ga jami’an duba makarantu a ƙananan hukumomi 27.
Wannan zai ƙarfafa ingancin koyarwa da kuma sa ido mai inganci a matakin farko da na sakandare.
Hon. Sagir Musa Ahmed, Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, ya tabbatar da cewa waɗannan matakai sun yi daidai da shirin gwamnati mai ƙudirai 12 wajen bunƙasa ilimi, noma, ci gaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook