Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na naira biliyan 75 a shekarar 2025, domin gabatar da shi ga majalisar dokokin jihar.
Wakilinmu ya tattaro daga Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa, wanda ya yi magana bayan taron majalisar zartarwa a Dutse na ranar Talata.
Ya ce ƙarin kasafin ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga da gwamnati ta samu.
“Za a raba kasafin tsakanin gwamnatin jiha (naira biliyan 58) da kuma ƙananan hukumomi 27 (naira biliyan 17). Wannan zai ƙunshi kuɗaɗen gudanarwa da na manyan ayyuka,” in ji Musa.
Dalilin ƙarin kasafin
Kwamishinan ya ce manufar ƙarin kasafin ita ce ƙarfafa sassa masu muhimmanci kamar ilimi, kiwon lafiya, noma da gine-gine, tare da tallafa wa sababbin buƙatu da ba a hango ba.
In za a iya tunawa a ranar 1 ga Janairu 2025, Gwamna Umar Namadi ya rattaba hannu kan babban kasafin kuɗi na naira biliyan 698.3, mafi girma a tarihin jihar.
Namadi ya ce kasafin na bana ya fi karkata ga manyan ayyuka, inda sama da kashi 76% aka ware domin fannin.
“Ina ganin wannan kasafi zai gina harsashin ci gaban tattalin arziƙi da inganta rayuwar jama’a a nan gaba,” in ji Gwamnan na Jigawa.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook