Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnatin Tarayya ta sake fitar da gargaɗi kan yiwuwar samun ambaliya a jihohi 14 ciki har da Legas, Adamawa, da wasu garuruwa 52.
Wannan gargaɗi na ƙunshe ne a hasashen ambaliya da Cibiyar Faɗakarwa Kan Ambaliya (National Flood Early Warning Centre) ta fitar ranar Talata, ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, inda aka bayyana cewa ana sa ran samun ruwan sama mai yawa tsakanin 16 zuwa 18 ga Satumba, 2025.
Rahoton da wakilinmu ya tattara daga ma’aikatar ya nuna cewa daraktan sashen Kula da Zaizayar Ƙasa, Ambaliya and Yankin Gaɓar Ruwa, Usman Abdullahi Bokani, ne ya sanya hannu kan sanarwar.
Jihohin da abin ya shafa
Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ambaliya sun haɗa da:
- Akwa Ibom (Upenekang, Eket, Oron, Uyo da sauransu),
- Anambra (Ogbakuba, Nnewi),
- Adamawa (Yola, Wuro Bokki, Jimeta),
- Cross River (Calabar, Akpap),
- Bayelsa (Yenagoa, Amasoma, Sagbama, Otuoke da sauransu),
- Delta (Asaba, Patani, Escravos),
- Kaduna (Kachia, Kauru),
- Kebbi (Birnin Kebbi, Kalgo),
- Katsina (Bakori),
- Rivers (Bonny, Ahoada, Bori),
- Imo (Egbema, Oguta),
- Sokoto (Argungu, Silame),
- Ondo (Ore, Igbokoda, Okitipupa),
- Lagos (Epe).
Matakan gaggawa
Wakilinmu ya gano cewa tun a ranar Talata, Adamawa ta fara jin tasirin ruwan sama da aka yi tun daga ƙarfe 4 na safe har zuwa ƙarfe 12 na rana.
Hukumar NEMA ta tabbatar da ambaliyar da ta shafi garuruwa 13 a ƙananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu.
A wata sanarwa da NEMA ta wallafa a shafin X, hukumar ta ce, “Mun haɗa kai da hukumar ba da agajin gaggawa ta Adamawa (ADSEMA), jami’an kashe gobara na tarayya da na jiha, jami’an tsaro da ma’aikatan sa kai wajen gudanar da aikin ceto da kwashe jama’a daga yankunan da ruwa ya shafa. An mayar da su wuraren da aka tanada na wucin gadi domin tsaro da kariya.”
A Legas, wakilinmu ya sami rahoton cewa ruwan sama na makon jiya ya haddasa cunkoson ababen hawa a hanyar Ikorodu, musamman daga Anthony zuwa gadar Odo-Iyalaro, inda direbobi da fasinjoji suka maƙale.
Gwamnati ta buƙaci jama’a, musamman mazauna ƙananan hukumomin da ke bakin koguna, da su ɗauki matakan kariya tare da yin taka-tsantsan don guje wa asarar rayuka da dukiyoyi.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook