Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta yi gargaɗin cewa jihohi 11 na iya fuskantar ambaliyar ruwa mai tsanani daga ranar 14 zuwa 18 ga Satumba 2025.
Wakiliyarmu ta tattaro daga sanarwar cibiyar hasashen ambaliyar ruwa ta ƙasa cewa, jihohin da abin zai shafa sun haɗa da Adamawa, Benue, Nasarawa, Taraba, Delta, Niger, Kebbi, Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara.
Sanarwar ta kuma nuna cewa ƙarin samun ruwa a kogin Gongola, Benue da Neja zai iya haddasa mummunar ambaliyar da ke barazana ga al’umman da ke bakin koguna.
“Al’ummar da ke bakin kogin Gongola da Benue zuwa Lokoja su gaggauta barin wuraren domin kauce wa ibtila’i,” in ji sanarwar.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ambaliyar ruwa a Zariya, Jihar Kaduna, da ta rusa gidaje sama da 270 tare da raba mutane fiye da 470 da muhallinsu.
Rahoton hukumar NEMA ya nuna cewa daga Janairu zuwa farkon Satumba 2025, ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 231 a Najeriya, yayin da 114 suka ɓata, wasu 607 kuma suka samu raunuka.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook