Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da dawo da darasin Tarihi a matsayin darasi na dole a makarantun firamare da sakandire.
Wannan mataki, a cewar ma’aikatar ilimi ta tarayya, na da nufin ƙarfafa kishin ƙasa, haɗa kan al’umma da kuma samar da ƴan ƙasa masu nagarta.
Sanarwar da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa ɗalibai za su fara koyon Tarihi daga aji ɗaya na firamare har zuwa aji uku na sakandiren farko, yayin da ɗaliban sakandiren gaba za su yi sabon darasin Civic and Heritage Studies, wanda ya ƙunshi haɗakar Tarihi da Darasin Harkokin Zamantakewa.
Wakilinmu ya tuno cewa a shekarar 2009/2010 aka cire Tarihi daga kundin karatun firamare da sakandire, bayan an ƙaddamar da sabon tsarin New Basic Education Curriculum.
A wancan lokacin an bayar da hujjar cewa ɗalibai ba sa sha’awar darasin, malamai kuma sun yi ƙaranci.
Sai dai a shekarar 2017 aka fara shirin mayar da shi, sannan a 2022 aka ƙaddamar da horar da malamai domin shirya makarantun ƙasar ga wannan sabuwar manufa.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook