Gwamnati ta ƙaddamar da sabon tsari don sauƙaƙa takin zamani ga manoma a Najeriya

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Shirin Taki na Ƙasa (PFI) ya bayyana cewa yana ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da wadataccen taki ga manoma a Najeriya, domin ciyar da manufofin Shugaba Bola Tinubu na samun cikakkiyar cin gashin kai a abinci.

Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar shugaban shirin, Tajudeen Ahmed, cewa yanzu PFI ya shiga sabon mataki na PFI 3.0 wanda zai tabbatar da wadatattun kayayyakin haɗa taki, tare da gina tsarin dogaro da kai.

“Tun daga watan Satumba 2025, mun riga mun samu kuma mun tsara samun kayayyakin fiye da waɗanda aka samar a 2024. An gama yarjejeniya da masu samar da albarkatun taki don cika rumbunan ajiya a fadin ƙasar,” in ji sanarwar.

Ci gaba a samar da kayayyaki

Sanarwar ta MOFI ta nuna cewa daga 2022 zuwa 2025, jiragen ruwa 48 sun kawo manyan kayayyakin haɗa taki ƙarƙashin shirin.

A bana kaɗai, an sauƙe fiye da tan 560,000 na kayayyakin taki daga jiragen ruwa 10 a tashoshin ruwa na Najeriya.

Dr. Armstrong Takang, shugaban MOFI, ya bayyana cewa PFI na nufin kare manoma daga tashin farashin kasuwannin duniya.

“Muna gina tsarin da zai tabbatar da ɗorewar samar da taki ba tare da tasirin kasuwar duniya a kansa ba,” in ji shi.

Fa’idoji ga manoma

An bayyana cewa shirin ya samar da taki fiye da buhuna miliyan 128 tun kafa shi, inda yanzu akwai fiye da masana’antu 90 na haɗa taki a Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar Masu Haɗa Taki (FEPSAN), Alhaji Sadiq Kassim, ya ce “An samu ci gaba a ƙarfafa masana’antu. Yanzu muna da ƙarfin samar da tan miliyan 13 a shekara, abin da ya kawo taki kusa da manoma da rage kuɗin sufuri.”

Ko da yake farashin taki ya tashi a wasu lokuta, masana sun danganta lamarin da tashin farashin dalar Amurka da kayayyakin da ake shigo da su daga waje.

An bayyana cewa daga watan Nuwamba 2025, MOFI za ta karɓi alhakin gudanar da shirin daga NSIA, a matakin PFI 3.0, wanda zai ƙarfafa sa ido, samar da taki a ko da yaushe da kuma rage matsalar ɓoyewa ko karkatar da kayayyakin taki.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

ManomaNomaTakin Zamani
Comments (0)
Add Comment