Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada matsayin gwamnatin jihar kan shan giya, yana mai bayyana cewa dokar ba wai an tsara ta ba ne domin tauye haƙƙin wani, illa dai domin daidaita lamuran da suka saɓa wa doka, al’ada da addini.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis yayin wani shirin tattaunawa kai tsaye na “Beyond The Headlines” a tashar talabijin ta TVC.
A yayin shirin, Namadi ya taɓo batutuwa da dama da suka shafi siyasa, ilimi, noma da ayyukan raya ƙasa, sannan ya yi ƙarin haske kan dokokin jihar tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2023.
“Dokar Hisbah mun sake dubawa ne tare da shigar da ra’ayin jama’a. Ba ta tauye haƙƙin kowa ba. Ta shafi abubuwan da suka saɓawa dokokinmu, al’adunmu da addininmu,” in ji gwamnan.
Da aka tambaye shi game da yadda dokar ta shafi waɗanda ba Musulmi ba, Gwamna Namadi ya bayyana cewa doka ta shafi kowa, domin an haramta shan giya a fili ga kowa da kowa.
“Shan giya a bainar jama’a an hana shi, ko Musulmi ne ko ba Musulmi ba. Ba za ka iya sha a parlour ko a fili ba, amma idan a cikin gida ne, daban ne. Abinda doka ta hana shi ne shan giya a bainar jama’a,” in ji shi.
Kazalika, gwamnan ya taɓo cece-kuce da ake yi kan siyan motocin ofis ɗinsa, inda ya ce gwamnati ta sayi motocin da suka dace da matsayin ofishin gwamna.
Ya ce farashin motocin bai kai biliyan ɗaya da miliyan ɗari takwas da ake yaɗawa ba.
“Ban sayi mota ba lokacin da na hau kujerar gwamna. Duk motocin da muka saya ba su wuce naira miliyan 400 ba, ba biliyan 1.8 kamar yadda ake yaɗa jita-jita ba. Gwamnatin Jigawa tana aiki da gaskiya da gaskiya a dukkan al’amuranta,” in ji shi.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook