DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya gabatar da “kasafin ƙarfafawa, sabunta juriya da wadata ga kowa” na 2026 mai yawan naira tiriliyan 58.47

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin Tarayyar Najeriya na shekarar 2026, wanda ya kai jimillar naira tiriliyan 58.47, ga zaman haɗin gwiwar Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, inda ya jaddada cewa kasafin ya mayar da hankali kan tsaro, ci gaba mai ɗorewa da walwalar jama’a.

Shugaban Ƙasar ya gabatar da kasafin ne a ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa kuɗaɗen manyan ayyuka (capital expenditure) sun kai naira tiriliyan 26.08, yayin da kuɗaɗen al’amuran yau da kullum da babu bashi a cikinsu (recurrent non-debt expenditure) suka tsaya a naira tiriliyan 15.25.

A cewarsa, kasafin ya dogara ne da hasashen farashin gangar ɗanyen mai a kan dala $64.85, tare da samar da mai ganga miliyan 1.84 a rana, da kuma canjin kuɗi na ₦1,400 kan kowace dala ɗaya ta Amurka a shekarar kasafin ta 2026.

Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa ana sa ran samun kuɗaɗen shiga da suka kai naira 34.33, yayin da jimillar kashe kuɗaɗen gwamnati aka ƙiyasta su a naira tiriliyan 58.18.

Daga cikin wannan adadi, an ware naira tiriliyan 15.52 domin biyan bashin da ake bin ƙasar.

Tinubu ya kuma bayyana cewa giɓin kasafin ya kai naira tiriliyan 23.85, wanda ya kai kashi 4.28 cikin 100 na Jimillar Tattalin Arziƙin Ƙasar (GDP).

Dangane da rabon kasafin ga sassa daban-daban, tsaro da kare ƙasa sun samu mafi girman kaso, inda aka ware musu naira tiriliyan 5.41, abin da ke nuna ƙudirin gwamnati na magance matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.

Ɓangaren ababen more rayuwa ya biyo baya da naira tiriliyan 3.56.

Ɓangaren ilimi ya samu naira tiriliyan 3.52, yayin da aka ware naira tiriliyan 2.48 ga ɓangaren lafiya, a cikin kasafin da aka sanya wa suna “Kasafin Ƙarfafawa, Sabunta Juriya da Wadata Ga Kowa” (Budget of Consolidation, Renewed Resilience and Shared Prosperity).

Yayin da yake jawabi ga ƴan majalisar, Shugaban Ƙasar, tsohon gwamnan Jihar Legas, ya jaddada cewa kasafin ba wai kawai jerin lambobin kuɗi ba ne.

“Waɗannan ba wai layukan lissafi kaɗai ba ne,” in ji Tinubu, “Su ne bayyanannen saƙo na manyan muradun ƙasa.”

Ya ƙara da cewa: “Muna nan daram wajen tabbatar da daidaiton kuɗin gwamnati, gaskiya a harkar bashi, da kuma kashe kuɗin jama’a ta hanyar da za ta samar da ƙima mai ma’ana.”

TIMES HAUSA ta fahimci cewa ƙudirin kasafin na 2026 zai shiga matakin nazari da tattaunawa a Majalisar Ƙasa, kafin amincewa da shi a hukumance, yayin da ake sa ran ƴan majalisa za su yi nazari kan manyan abubuwan da suka shafi tsaro, ci gaban tattalin arziƙi da jin daɗin ƴan Najeriya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Kasafin KudiTinubu
Comments (0)
Add Comment