Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Wakilan Jihar Borno da Kano, Musa Ahmed Musa da Hafsat Sada, sun zama zakarun Gasar Karatun Al-Ƙur’ani Maigirma ta Najeriya karo na 40 a rukunin maza da mata, lamarin da ya jawo farin ciki da yabo daga sassa daban-daban na ƙasar.
An sanar da sakamakon gasar ne a ranar Asabar a birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ta bakin Daraktan Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, Farfesa Abubakar Yelwa.
Gasar, wadda ta ɗauki tsawon mako guda, ta haɗa ƴan takara 296 daga jihohi 30 na ƙasar, inda suka fafata a rukunai shida na karatun Al-Ƙur’ani da haddarsa.
Da yake jawabi a wajen bikin rufe gasar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa nasarar gudanar da gasar ta shekarar 2025 alama ce ta dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ya ce gasar ta nuna jajircewar al’ummar Borno wajen zaman lafiya, ilimi da neman sani.
“Karɓar baƙuncin wannan gagarumin taro karo na 40 ba kawai karramawa ba ce ga Jihar Borno, alama ce ta tsayayyen ƙudurinmu na tabbatar da zaman lafiya, inganta ilimi da kuma neman ilimin addini, musamman hikimar da ke cikin Al-Ƙur’ani Mai Girma,” in ji Zulum.
Gwamnan ya ƙara da cewa, “Jihar Borno na nan daram wajen sake gina al’umma, dawo da zaman lafiya da fifita ilimi, na zamani da na addini. Nasarar gudanar da wannan gasa saƙo ne a fili ga duniya cewa Borno ta dawo, Borno lafiya take, kuma Borno cibiyar ilimi da bunƙasar addini ce.”
Zulum ya taya zakarun gasar da sauran ƴan takara murna, yana mai cewa nasararsu ba wai lashe kyauta kaɗai ba ce, illa sakamakon jajircewa, ladabi da girmama Kalmar Allah.
“Duk wanda ya halarci wannan gasa nasara ya samu, domin ruhin gasar na cikin neman ilimi da jarumtakar tsayawa a gaban alƙalan gasar,” a jaddadawarsa.
Gwamnan ya kuma nuna godiya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da uwargidansa Hajiya Nana Kashim Shettima, gwamnonin jihohi da mataimakansu, sarakunan gargajiya, Jami’ar Usman Dan Fodio, da sauran manyan baƙi da suka tallafa wajen nasarar taron.
Bikin ya samu halartar uwargidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Dikko Umaru Radda, Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, da sauran sarakuna, ƴan majalisun tarayya da jihohi, mataimakin shugaban APC na ƙasa, kwamishinoni, malamai da sauran manyan baƙi.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook