Badaƙalar Cin Hanci A Kano Ta Kara Ƙazanta, Kwamishina Ya Amince Da Yin Badaƙalar Naira Biliyan 1.17

Badaƙalar cin hanci a gwamnatin Kano ta ƙara muni bayan Kwamishinan Harkokin Al’umma da Ci Gaban Ƙauyuka na jihar, Abdulkadir Abdulsalam, ya amince da cewa ya sanya hannu a kan biyan kuɗi har Naira biliyan 1.17 da ba a yi kwangilar da aka ce za a yi ba, lokacin yana Babban Akawuntan jihar.

Wakilinmu ya gano daga takardun ICPC cewa, Abdulsalam ya amince da biyan kuɗin a watan Nuwambar 2023 don kwangilar da babu ita a ainihi.

Masu bincike sun ce wannan biyan ya zama wani ɓangare na zargin karkatar da Naira biliyan 6.5 ta hanyar haɗa baki da manyan jami’an gwamnati da masu canjin kuɗi.

Shaidun da aka samu sun nuna cewa, an cire kuɗin ne daga asusun gwamnati, aka juya su zuwa daloli, sannan aka kai wa Abdullahi Rogo, Daraktan Al’amuran Fadar Gwamna Abba Yusuf, a Abuja.

ICPC ta ce ta riga ta dawo da Naira biliyan 1.1 daga cikin kuɗin.

Gwamnatin Yusuf ta bayyana rahotannin cin hanci a matsayin na “ƙarya” daga abokan hamayyarta.

Amma ƙaruwar samun shaidu kan laifin na tunatar da wasu badaƙalolin da suka shafi tsofaffin gwamnatocin Kano, ciki har da zargin cin hanci da ruf da ciki da suka shafi Abdullahi Ganduje, Rabiu Kwankwaso da Ibrahim Shekarau.

Lamarin na ƙara ƙarfafa kira ga hukumomin Kano da su fitar da cikakken bayani kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen jama’a, musamman a wannan lokacin da ake sa ido sosai kan gaskiyar gudanar da mulki a jihar.

Abba Kabir YusufCin HanciICPCKano
Comments (0)
Add Comment