Atiku ya karɓi ƴan tsohuwar CPC, ya caccaki gwamnatin Tinubu kan dokar ta ɓacin Jihar Rivers

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya karɓi shugabannin jihohi na tsohuwar jam’iyyar CPC a gidansa da ke Abuja, inda suka shaida masa goyon bayansu ga yunƙurinsa na ceto Najeriya daga rikicin da yake ganin gwamnatin APC mai ci ta jefa ƙasar.

Atiku ya bayyana a shafinsa na X cewa shugabannin CPC sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kauce daga manufofin farko na kishin talakawa da jam’iyyar APC ta fara da su.

Ya ce ya yi amfani da wannan taro wajen bayyana musu yadda ake ƙoƙarin kafa sabuwar tafiyar siyasa mai suna African Democratic Congress, wanda ya bayyana a matsayin dandalin jama’a da zai sake dawo da ƙwarin gwiwa ga ƴan kasa.

Atiku ya kuma buƙace su da su ƙarfafi masu goyon bayansu wajen yin rajistar zaɓe a yanzu, domin a cewarsa, wannan shi ne matakin farko na tabbatar da nasarar tafiyar.

A wani saƙo daban da ya wallafa, Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan batun dakatar da gwamna Simi Fubara na Jihar Rivers da majalisar dokokin jihar.

Ya bayyana cewa cire dakatarwar ba abin murna ba ne domin tun farko dakatar da gwamnati da ƴan majalisa ya saɓawa doka.

Ya ce Shugaba Tinubu ba shi da ikon dakatar da gwamnoni ko majalisun jihohi da aka zaɓa cikin tsarin demokaraɗiyya, yana mai bayyana lamarin a matsayin alamar mulkin kama-karya na gwamnatin da ke ci.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Atiku Abubakar
Comments (0)
Add Comment