Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jagoran adawa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ɗauki nauyin karatun ƴan mata uku da suka lashe gasar TeenEagle Global Finals ta Turancin Ingilishi da aka gudanar a Ingila.
BBC Hausa ta tattaro a wata sanarwa da Gidauniyar Atiku ta fitar ranar 5 ga watan Agusta cewa, an bayyana nasarar Nafisa Abdullahi, Rukaiya Mohammed Fema, da Khadija Kashim Kalli a matsayin ƴan manuniyar cewa “kowanne yaro na iya cimma burinsa.”
A cewar sakataren gidauniyar, Farfesa Ahmadu Shehu, “A matsayinsu na gwarazan gasar, Gidauniyar Atiku Abubakar za ta ɗauki nauyin kammala karatun sakandare har zuwa jami’a a kowace jami’a da suka zaɓa.”
Rahotanni sun nuna cewa matasan, waɗanda dukkansu ƴan asalin Jihar Yobe ne, sun doke abokan takara 20,000 daga sassan duniya daban-daban bayan sun wakilci Najeriya daga makarantar Tulip International College.
A wani saƙo da Atiku ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ɗaliban, Nafisa Abdullahi, ta kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja ranar Alhamis.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook